1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

February 17, 2006

Dari-dari da kasashen Turai ke yi wajen Tura sojojinsu zuwa kasar Kongo shi ne ya dauki hankalin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvQ3

Daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin jaridun Jamus a rahotannin da suka bayar dangane da nahiyar Afurka shi ne shawarar tura sojojin kwantar da tarzoma na kasashen Kungiyar Tarayyar Turai (KTT) zuwa Kongo. Kawo yanzun dai kusan dukkan kasashen kungiyar na daridari da rokon gudummawar soja da MDD ta gabatar musu in ji jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG wacce ta kara da cewar:

“Kawo yanzu babu wata kasa daga cikin gaggan kasashen KTT da ta bayyana shirinta na jagorantar rundunar ta kiyaye zaman lafiya, wadda MDD ta bukata, domin tabbatar da nasarar zaben shugaban kasar Kongo da aka shirya gudanarwa nan gaba a wannan shekara. A nata bangaren Jamus ta ce tana jira ne ta samu cikakkun bayanai a game da irin alhakin da za a dora wa rundunar. Amma rahotanni sun ce tuni aka gabatar da wadannan bayanai, illa kawai ita Jamus so take a yi mata karin bayani bisa manufa.”

Ita ma jaridar DIE TAGESZEITUNG ta tofa albarkacin bakinta akan manufar inda take cewar:

“Ga alamu dai kasashen Turai tsoro suke da su tura sojojinsu zuwa kasar Kongo domin sa ido akan zaben demokradiya na farko da aka shirya gudanarwa a wannan kasa. Jami’an diplomasiyyar kasashen kungiyar sun bayyana shakkunsu a game da tsugunar da sojojin, wadanda ainifin alhakin da za a dora wa sojojin na kwantar da tarzoma daga kasashen Turai shi ne tsaron filayen jiragen sama da iyakoki da sauran wurare masu mhummanci a fadar mulki ta Kinshansa.”

A halin da muke ciki yanzu haka daya daga cikin manyan tafkunan nahiyar Afurka na fuskantar barazanar gushewa daga doron kasa baki daya. Wannan maganar kuwa ta shafi tafkin Chadi ne dake tsakanin Nijeriya, Nijer da Kamaru da kuma kasar Chadi. A lokacin da take bitar wannan matsala jaridar BERLINER ZEITUNG cewa tayi:

“Tafkin Chadi da a da can ya fi kowane girma a yammacin Afurka na fuskantar barazanar gushewa kwata-kwata daga taswirar duniya, inda duka-duka zurfinsa a yanzun bai wuce mita daya da rabi ba. A zamanin da a misalin shekaru dubu biyu da dari biyar da suka wuce girman tafkin ya kai fadin harabar kasar Jamus, amma sannu a hankali ya rika raguwa zuwa fadin jihar Northrhine-Westfaliya a wajejen shekara ta 1960. A halin yanzu kuwa duka duka fadin sa bai wuce girman birnin Berlin ba.”

Ga alamu kasashen yammaci sun gaza a kokarin da ake yi na shawo kan rikicin lardin Darfur, wanda ya halaka mutane sama da dubu 300, in ji jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG, wadda ta kara da cewar:

“Koda-da-kowa ya san mawuyacin halin da ake ciki a lardin Darfur na yammacin kasar Sudan, inda a cikin watan janairun da ya wuce kawai aka fatattaki mutane kimanin dubu 30 daga yankunansu na asali. Daga baya-bayan nan ma rikicin na neman rutsawa da makobciyar kasa ta Chadi. Abun takaici ne ganin yadda duniya ta zauna sasakai tana mai zura ido akan ta’asar dake faruwa a wannan lardi ba tare da ta tabuka kome ba.”