1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

January 20, 2006

Halin da ake ciki a Cote d'Ivoire shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan makon

https://p.dw.com/p/BvQ7
Tashe-Tashen hankula a Abidjan
Tashe-Tashen hankula a AbidjanHoto: AP

A dai wannan makon muhimman batutuwan da suka fi daukar hankalin masharhanta na jaridu da mujallun Jamus sun hada ne da halin da ake ciki a kasar Cote d’Ivoire da rikicin yankin delta na Nijeriya da kuma shirin taron kolin kungiyar tarayyar Afurka a Khartoum ta kasar Sudan tare da ba da la’akari da halin da ake ciki a lardin Darfur..Amma da farko zamu fara ne da rahoton jaridar DIE TAGESZEITUNG a game da yadda ‘yan tawaye ke ta da zaune tsaye a yankunan hakan man Nijeriya. Jaridar sai ta ce:

“Wata kungiya mai kiran kanta wai kungiyar wayar da kan al’umar Niger-Delta (MEND) a takaice ta lashi takobin saka kafar wando daya da dukkan kamfanonin dake hakan mai a yankin Niger-Delta. A sakamakon hare-haren da aka kai kan kafofinsa guda uku a makon da ya gabata kamfanin Shell ya kwashe ma’aikatansa sama da dari uku abin da ya kai ga kayyade yawan mai da kamfanin ya saba hakowa na garewani dubu 900 a rana. Kawo yanzun dai ba wanda ya san tahakikanin wannan kungiya ta MEND da kuma manufar da ta sa gaba.”

Al’amura sai dada yin tsamari suke yi a kasar Cote d’Ivoire ta yammacin Afurka, inda a wannan makon magoya bayan shugaba Laurent Gbagbo suka kai farmaki kan sansanin sojan kiyaye zaman lafiya na MDD a birnin Abidjan sakamakon kiran da shugaban yayi na janyewar dakarun majalisar daga wannan kasa. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta rawaito rahoto akan haka tana mai cewar:

“Wadannan tashe-tashen hankula da kuma janyewar da jam’iyyar FPI tayi daga gwamnatin rikon kwaryar da aka nada tamkar wani babban koma baya ne ga sabon P/M Charles Konan Banny. Domin kuwa ba kawai tsoro ake na cewar a yanzu ba ya da ikon shawo kan mawuyacin halin da ake ciki ne ba, kazalika an fargabar sake barkewar wani sabon zagaye na yakin basasar kasar Cote d’Ivoire mai arzikin koko a yammacin Afurka.”

Ita ma jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi bitar halin da ake ciki a Cote d’Ivoire tare da bayar da la’akari da wani rahoton da kungiyar tarayyar Turai ta bayar wanda ke amfani da ribar da kasar ke samu daga cinikin koko domin sayen makamai. Jaridar sai ta kara da cewar:

“Duk mai sayen coklat a halin yanzu yana taimakawa wajen kara rura wutar rikicin kasar Cote d’Ivoire. Magabatan kasar sune suka yi kane-kane a harkar noma da cinikin koko, wanda suke amfani da ribarsa domin sayen makamai da kuma arzuta kansu da kansu. Ita dai Cote d’Ivoire, ita ce lamba wan wajen cinikin koko a duniya, inda take noma kashi 40% na koko da ake cinikinsa a kasuwannin duniya.”

A can kasar Togo kuwa ko da yake dan kama karyar ya mutu, amma har yau tana ci gaba da fama da mulkin kama karya in ji jaridar NEUES DEUTSCHLAND, wadda ta ci gaba da cewar:

“Tun bayan da Faure Eyadema dan marigayi Gnassingbe Eyadema ya gaji karagar mulki daga mahaifinsa al’amura ke dada yin tsamari a kasar Togo. A halin yanzu haka dakarun sa kai na gwamnati na kai da komo a manyan birane da garuruwan kasar a cikin fararen kaya tare da barazana ga iyalan abokan adawar gwamnati. Kai hatta ‘yan kasar Togo da suka tsrere domin neman mafaka a makobciyar kasa ta Benin ba su tsira daga daga ta’asar dakarun na Faure Eyadema ba. A shekarar da ta gabata ma sai da dan kama karyar ya raba wa dakarun nasa makamai saboda tsoron barkewar yakin basasa a kasar ta yammacin Afurka.”

Kasar Sudan mai karbar bakuncin taron kolin kungiyar tarayyar Afurka na bana ta dage akan lalle sai an danka mata ragamar shugabancin kungiyar kamar yadda aka saba bisa al’ada. Bisa ga ra’ayin jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG dai dalilin wannan dagewar shi ne:

“Domin ta haka gwamnatin shugaba El-Bashir dake shan tofin Allah tsine sakamakon ta’asar kisan kiyashi a lardin Darfur zata iya yin amfani da wannan dama domin wanke sunanta da kuma neman daga martabarta a idanun kasashen Afurka. Wani abin mamaki kuwa shi ne, in banda shugaba Idris Deby na kasar Chadi da suka shiga takun-saka da Sudan, ba wani shugaba na wata kasa a Afurka da ya bayyana damuwarsa game da haka.”