1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

January 13, 2006

Barazanar yunwa a gabacin Afurka ita ce tafi daukar hankalin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvQ8
Koma bayan noma a Kenya
Koma bayan noma a KenyaHoto: dpa - Report

A wannan makon dai babban abin da ya fi daukar hankalin jaridu da mujallun Jamus dangane da al’amuran Afurka shi ne mawuyacin hali na yunwa da ake fama da shi a gabacin Afurka, inda misali a kasar Kenya aka kiyasce cewar mutane miliyan biyu da rabi ne ke bukatar taimakon abinci a wannan kasa yanzu haka. Amma da farko zamu duba dangantakar China ne da kasashen Afurka ta la’akari da balaguron kasashen Afurka da ministan harkokin wajen Chinar ke yi yanzu haka. A cikin nata sharhin a game da wannan balaguro jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

“Manufar ziyarar ministan harkokin wajen kasar China ga kasashen yammacin Afurka shi ne domin cimma yarjeniyoyin cinikin albarkatun kasa da kasashen da lamarin ya shafa. Tun kafin tashinsa ministan harkokin wajen zuwa yammacin Afurka ne aka cimma wata gagarumar yarjejeniya dake ba wa kamfanonin China damar hakan man fetur a gabar tekun Nijeriya akan dalar Amurka miliyan dubu biyu da dari uku. Kasar tana China tana bukatar albarkatun kasa daga kasashen Afurka, kamar dai man fetur da katako dangane da bunkasar tattalin arzikin da take samu a cikin gaggawa. Dangane da kasashen na Afurka kuwa suna marhaban lale da kasar China a matsayin wata abokiyar burmin ciniki fiye da kasashen yammaci, saboda ba ta shimfida musu ire-iren sharuddan nan na rungumar Demokradiyya ko girmama hakkin dan-Adam da yakar cin hanci da dai makamantansu.”

Ana fama da mawuyacin hali na fari a shiyyar gabacin Afurka, inda aka kiyasce cewar mutane miliyan goma sha daya ne ke fama da radadin yunwa a wannan yanki yanzu haka. A lokacin da take gabatar da wannan rahoto jaridar NEUES DEUTSCHLAND cewa tayi:

“Alkaluma sun nuna cewar mutane miliyan shida ne suka dogara kacokam akan taimakon abinci daga ketare a kasashen Somaliya da Muzambik da Kenya da kuma Jibuti.”

Ita ma jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta rawaito wannan rahoto tana mai dora laifin wannan mawuyacin hali akan magabatan kasashen da lamarin ya shafa. Jaridar ta ambaci wakiliyar kungiyar taimakon abinci ta Jamus Welthungerhilfe tana mai bayanin cewar:

“Sakaci na magabatan kasashen da lamarin ya shafa shi ne umma’aba’isin wannan hali na yunwa da ake ciki. Misali kasar Kenya wacce a yanzu haka take da mutane kimanin miliyan biyu da rabi dake fuskantar barazanar yunwa, tun da dadewa aka hangi matsalar domin kuwa kasar ta dade tana fama da karancin ruwan sama, kuma a sakamakon haka aka fara kada gangami game da barazanar da ka biyo baya tun a shekara ta 2004. Amma ba wanda ya saurari wannan gargadi, walau gwamnatin Kenya ko kasashen yammaci dake ba da taimako.”

Kasashen Kungiyar Tarayyar Turai sun tsayar da shawarar fuskantar wata sabuwar alkibla dangane da manufofinsu dangane da ‘yan gudun hijira, in ji jaridar ciniki ta Handelsblatt a cikin wani sharhin da ta gabatar ta kuma kara da cewar:

“Wannan sabuwar alkiblar mai tsanani da KTT ke so ta fuskanta tamkar mayar da martani ne akan rikicin ‘yan gudun hijirar da ya addabi kasashenta a baya-bayan nan. A maimakon niyyarta ta kafa sansanonin karbar ‘yan gudun hijira a kasashen Afurka a yanzu kungiyar ta tsayar da shawarar taimaka wa kasashen da lamarin ya shafa tare da kyautata hanyoyin musayar rahotanni tsakaninsu ta yadda za a samu kafar dakatar da tuttudowar dubban ‘yan gudun hijirar zuwa nahiyar Turai.”

Yau kimanin shekara daya ke nan da aka cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin gwamnatin Sudan da ‘yan tawayen kudancin kasar. Jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta duba sakamakon wannan yarjejeniya a tsakanin watanni 12n da suka wuce sai ta ce:

“A hakika babu wani sauyin da aka samu tun bayan raba madafun iko da aka yi a fadar mulki ta Khartoum. Akwai masu ikirarin cewar ainifin take-taken wasu masu fada a ji daga bangaren masu fada a ji na arewacin kasar na da nufin yi wa ‘yan kudancin Sudan kora da hali ne ta yadda lamarin zai kai musu iya wuya su janye daga gwamnatin domin ballewa daga Sudan baki daya.”