1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

December 9, 2005

Sabani tsakanin Eritrea da MDD na daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvQC
Tutar Eritrea
Tutar Eritrea

A wannan makon mai karewa dai jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni masu yawa akan al’amuran nahiyarmu ta Afurka. Misali shari’ar da aka kaddamar akan Ralph Uwazurike mai fafutukar neman ballewar lardin kabilar Ibo a karkashin sunan Biafra daga tarayyar Nijeriya. A lokacin da take ba da rahoto game da haka jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU cewa tayi:

“An fuskanci mummunar arangama tsakanin ‘yan sanda da wasu matasa a wasu yankunan kudancin Nijeriya a wannan makon sakamakon shari’ar da aka gabatar akan Ralph Uwazurike, wanda ya kafa wata kungiyar dake neman sake farfado da rikicin ballewar abin da ya kira wai ‘yantacciyar kasar Biafra daga tarayyar Nijeriya, Massob a takaice. Ana zargin Uwazurike da wasu mukarrabansa su shida da laifin kafa wata kungiya mai damarar makamai dake neman ballewar lardin kabilar Ibo da karfin hatsi. To sai dai kuma ko da yake dubban daruruwar mazauna yankunan kudancin Nijeriya suka shiga yajin aiki, amma ba tabbas a game da ko shin sun amsa kiran da kungiyar Massob tayi ne ko kuwa sun ki komawa bakin aikinsu ne saboda nuna rashin gamsuwarsu da salon kamun ludayin gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo.”

A can kasar Cote d’Ivoire an nada sabon P/M Charles Konan Banny, wanda kamar yadda shugabannin kasashen Nijeriya da Afurka ta Kudu, Obasanjo da Mbeki suka nunar za a dora masa alhakin neman sasanta tsanta tsakanin gwamnatin Gbagbo da ‘yan tawaye tare da shirya wani sabon zabe nan da watan oktoban shekara ta 2006. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ce ta ba da wannan rahoton ta kuma ci gaba da cewar:

“Dukkan ‘yan tawayen da manazarta al’amuran yau da kullum sun yi marhabin da nada Charles Konan Banny da aka yi tare da halarcin shugaba Gbagbo. Jami’in dake da shekaru 63 da haifuwa, wanda kuma yayi shekaru masu yawa a karkashin wata jam’iyyar hamayya a kasar Cote d’Ivoire, kwararren masani ne akan al’amuran kudi kuma ana yaba masa da sanin makama. Bisa ga ra’ayin shugaba Nijeriya Olusegun Obasanjo nadin Charles Konan Banny tamkar wata nasara ce ga illahirin al’umar kasar Cote d’Ivoire.”

A wannan makon an fuskanci mummunan sabani tsakanin MDD da gwamnatin Eritrea, wadda ta kori wasu daga cikin ma’aikatan majalisar daga harabar kasarta. A cikin rahoton da ta bayar game da haka jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZETUNG cewa tayi:

“Matakin korar da gwamnatin Eritrea ta dauka ya fi shafar ma’aikatan MDD ne daga kasashen Amurka da Kanada da Rasha da kuma na kasashen Kungiyar Tarayyar Turai. Bisa ga dukkan alamu kuwa gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin mayar da martani akan barazanar kakaba wa Eritrea takunkumi da kwamitin sulhu na MDD yayi idan har ta ci gaba da hana ruwa gudu ga ayyukan sojojin kiyaye zaman lafiya su 3200 da majalisar ta tsugunar a iyaka tsakaninta da kasar Habasha. A cikin watan oktoban da ya gaba ne Eritrea ta haramta wa jiragen sama masu saukar ungulu na sojan kiyaye zaman lafiya shawagi a samaniyarta kuma ta haka ba su da cikakken ikon sa ido akan abin dake faruwa a iyakar kasar da kasar Habasha.”

Ga alamu murna ta fara komawa ciki dangane da shugaba Yewori Museveni na kasar Uganda, wanda a zamanin baya ake yaba masa da kasancewa babban misali game da sabon yanayi na shugabanci da aka shiga a nahiyar Afurka. Domin kuwa a baya ga kwaskwarimar da yayi wa daftarin tsarin mulkin kasar domin samun kafar ci gaba da rike madafun iko, kazalika shugaban na kasar Uganda na bakin kokarinsa wajen murkushe ‘yan hamayya da ka iya zama barazana gare shi a lokacin zabe. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta ci gaba ne da cewar:

“A halin yanzu haka shugaba Museveni ya bari an tsare tsofon likitansa Kizza Besigye, wanda aka ce wa yana da kwayar HIV ake kuma tuhumarsa da yi wa wata mata fyade a shekarar 1997. Kazalika ana zarginsa da kasancewa dan kungiyar tawayen nan ta LRA dake ta da zaune tsaye a arewacin kasar Uganda.”