1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka a Jaridun Jamus

July 8, 2005

A wannan makon taron kasashen G8 shi ne ya fi daukar hankalin jaridu da mujallun Jamus dangane da shirinsu na yafe wa kasashen Afurka dimbim bashin dake kansu

https://p.dw.com/p/BvpA

A wannan makon dai kamar yadda aka tsammata tun farko taron kolin kasashen G8 da suka fi ci gaban masana’antu a duniya shi ne ya fi daukar hankalin kafofin yada labarai, ba ma a nan kasar ta Jamus kadai ba, har da sauran sassa na duniyar, musamman ma nahiyar mu ta Afurka, wadda, ita ce ta fi daukar hankalin taron na bana dangane da shirin yafe wa kasashen nahiyar dimbim basussukan dake kansu. Mujallar Der Spiegel dake fita mako-mako ta rubuta dogon sharhi akan manufar yafe basussukan da shirin taimakon farfado da tattalin arzikin Afurka, inda take cewar:

“Kamar yadda aka lura a zamanin baya, taimakon kudi kawai ba zai tsinana kome ba wajen ceto makomar Afurka da kawar da matsalar talaucin dake addabar kasashenta. Domin kuwa ainifin kasashen da suka fi samun taimako a zamanin baya sune kuma suka fi fama da matsalar talaucin yanzu haka. An dade da yawa daga al’umar Afurka na gabatar da kiran dakatar da irin wannan taimako, saboda ainifin kudaden taimakon su kan kwarara ne zuwa aljifan jami’an siyasa da sauran mahukunta ‘yan cin hanci da nuna son kai da kuma fafutukar arzuta kansu da kansu. Amma ainifin talakawan Afurka wannan taimako ba ya tsinana musu kome.”

An ji irin wannan ra’ayin a cikin wata hira da jaridar Süddeutsche Zeitung tayi da wani dan jarida mai suna Andrew Mwenda daga kasar Uganda, wanda ya ci gaba yana mai cewar:

“Wannan taimakon baya tsinana mana kome, kuma manufar yafe basussuka da P/M Birtaniya Tony Blair ke hada-hadar cimmawa, babban kuskure ne, saboda zai zama tamkar lasin ne ga magabatan kasashen Afurka su rika cin karensu ba babbaka tare da facaka da dukiyar talakawa, sannan a karshe sai a yafe musu a matsayin kasancewar hakan wani kin ji ne irin na matasa.”

Ita kuwa jaridar Frankfurter Rundschau, bisa ga ra’ayinta kasashen Afurka zasu samu wata ‘yar sararawa sakamakon matakin na yafe musu basussukan dake kansu, saboda ta haka zasu samu bunkasa iya gwargwado ga kasafin kudinsu. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

“Matakin da kasashen G8 suka dauka tun a cikin watan yunin da ya gabata na yafe wa wasu kasashen Afurka, kamar su Ghana da Mali da Burkina Faso da Benin basussukan dake kansu ya taimaka matuka ainun wadannan kasashe suka samu ‘yar sararawa ta yadda a yanzun zasu iya amfani da rarar da suka samu wajen tafiyar da shirye-shiryensu na raya kasa. Misali kasar Burkina Faso a yanzu zata yi tsumulmular abin da ya kai dalar Amurka miliyan 129, wadanda ta saba kashewa wajen mayar da basussukanta da kuma kudaden ruwa dake kansu a duk shekara. Muhimmin abin da ake bukata shi ne amfani da wadannan kudade ta hanyoyin da suka dace da kuma taka tsantsan ka da a sake fadawa cikin wani mawuyacin hali na dimbim bashi nan gaba.”

Bayan tafiyar hawainiya da aka sha fama da ita a zamanin baya a yanzu kasar Sudan na samun ci gaba sannu a hankali wajen kyautata makomar manufofinta na siyasa, in ji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a cikin wani dogon sharhin da ta rubuta bayan bitar halin da ake ciki a kasar ta Sudan da tayi. Jaridar sai ta kara da cewar:

“Ba zato ba tsammani al’amura sun fara canzawa suna masu daukar wani sabon salo a kasar Sudan, bayan da aka kusa fid da kauna game da makomar siyasar kasar da tayi shekara da shekaru tana fama da rikici da yake-yake na basasa a sassanta dabam-dabam. A wannan makon an cimma daidaituwa tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen Darfur akan wata yarjejeniyar da ake fata zata taimaka wajen kawo karshen rikicin lardin na yammacin Sudan da ya ki ci ya ki cinyewa, sannan a kuma gobe asabar idan Allah Ya kai mu gwamnatin wucin gadi zata kama madafun iko a karkashin sabon daftarin tsarin mulkin da zai fara aikinsa a daidai wannan rana. A makon da ya gabata gwamnati a fadar mulki ta Khartoum tayi afuwa ga fursinonin siyasa masu tarin yawa abin da ya hada har da dan hamayya Hassan Al-Turabi, wanda ya bayyana cewar ba zai shiga a dama da shi a gwamnatin ta hadin gambiza ba, amma zai ci gaba da ma’amalla da tsofuwar kungiyar tawayen dake da hannu a gwamnatin. Kazalika al-Turabi zai iya taka muhimmiyar rawa a yammacin Sudan, saboda an ce shi ne ya kirkiro kungiyar adalci dake tawaye a lardin Darfur.”