1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

June 17, 2005

Maganar yafe wa kasashen Afurka dimbim bashin dake kansu ita ce ta fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan makon

https://p.dw.com/p/BvpC

A wannan makon jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni da dama akan al’amuran nahiyarmu ta Afurka, ko da yake babban abin da ya fi daukar hankalinsu shi ne shawarar yafe wa kasashen Afurka ‘yan rabbana ka wadata mu dimbin bashin dake kansu da kasashen G8 suka tsayar. A lokacin da take sharhi akan haka jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:

“Wannan dai wani dan karamin mataki ne aka dauka akan wata hanya madaidaiciya. Domin kuwa wannan karimcin da kasashe masu ci gaban masana’antu suka nunar, ba kome ba ne illa wani yunkuri na neman daga martabarsu a idanun jama’a, saboda ita kanta maganar ta shafi wani adadi ne na kudi, wanda tuntuni suka fid da kaunar cewar za a iya mayar musu da su. Bugu da kari kuma ba zai haifar musu da wani gibi ba.”

A wani sabon ci gaba a wannan makon shugaba Thabo Mbeki na kasar ATK ya taka rawar gani inda ya kore mataimakinsa daga bakin aikinsa sakamakon laifuka na cin hanci, matakin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce abin koyi ne ga sauran kasashe. Jaridar sai ta ci gaba tana mai cewar:

“Ko da yake ‘yan hamayya da wakilan gwamnati sun tafa wa shugaba Mbeki a game da matakin da ya dauka na sallamar mataimakinsa Jacob Zuma, wanda a da can aka yi zaton shi ne zai shugabanci Afurka ta Kudu, amma fa tun a yanzu aka fara hangen mummunar barakar da wannan matakin zai haddasa a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar ANC dake mulki. Domin kuwa akwai da yawa daga cikinsu dake da ra’ayin cewar wannan mataki bai dace ba, ganin irin rawar da Zuma ya taka a fafutukar murkushe mulkin wariyar jinsi da kuma radadin da ya sha famar fuskanta abin da ya hada har da shekaru masu yawa a kurkuku sakamakon wannan fafutuka tasa. Ana dai zargin Zuma ne da karbar rashawa ta kwatankwacin Euro dubu 150.”

A can Janhuriyar Demokradiyyar Kongo ana fama da hali na zaman dardar sakamakon sabanin dake akwai tsakanin gwamnatin Kabila da wasu kungiyoyin da suka bijire wa gwamnatin a cewar jaridar Die Tageszeitung a cikin wani rahoton da ta bayar, inda ta ce kome mai iya faruwa ne a wannan kasa kama daga kisan kare-dangi zuwa ga kifar da gwamnatin shugaba Kabila. Jaridar sai ta kara da cewar:

“A halin da ake ciki yanzun jita-jita sai dada yaduwa take yi a Kinshasa, fadar mulkin kasar Kongo, a game da cewar ‘yan tawaye na wa dakarunsu damarar adduna samfurin Tramontina, kirar kasar Brazil. Kuma ko da yake a hakika ba wanda ya taba ganin wadannan adduna na Tramontina, amma da yawa daga mazauna birnin Kinshasa sun hakikance cewar akwai mutane masu tarin yawa dake mallakar wadannan adduna. A baya-bayan nan aka shiga raba kasidun dake kira ga jama’a da su ta da kayar baya su kai farmaki kan jami’an siyasa da iyalansu kafin ranar 30 ga watan yuni. Bisa ga ra’ayin hafsoshin sojan kiyaye zaman lafiya na MDD su kimanin dubu 16 da aka tsugunar a kasar ta Kongo, wannan ba kome ba ne illa wani yunkuri na tsokanar fada, a saboda haka ba abin da zasu iya yi illa su kare kansu su kuma zura ido su ga abin da zai faru nan gaba.”

Majalisar dokoki da gwamnatin rikon kwarya na kasar Somaliya na shirin komawa gida, kuma mai yiwuwa hakan ya taimaka a samu sararawar al’amura a kasar da rikicinta ya ki ci ya ki cinyewa a cewar jaridar Neues Deutschland cikin rahotonta dake cewar:

“Kusan dukkan wakilan gwamnatin kasar Somaliya sun hakikance cewar mayar da mazaunin gwamnati zuwa Somaliyar ne kawai zai taimaka kasar ta samu sararawar al’amuranta bayan da kasar tayi kusan shekaru goma sha biyar bata da gwamnati, tun bayan kifar da mulkin shugaba Siad Barre da aka yi a shekarar 1991. To sai dai kuma kawo yanzu ba wanda ya san tahakikanin wurin da za a yi wa gwamnatin mazauni, ko Ya-Allah a Mogadishu ko a Baidoa ko kuma wani wajen dabam.”