1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

May 27, 2005

Daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus dangane da Afurka har da zargin da ake wa tsofon shugaban Liberiya Charles Taylor da ma'amalla da kungiyar Al-Ka'ida

https://p.dw.com/p/BvpF

A wannan makon dai sabon halin da aka shiga a siyasar Jamus, sakamakon zaben jihar Northrhine-Westfaliya da aka gudanar ranar lahadi da ta shige, shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus, ko da yake sun gabatar da rahotanni iya gwargwado akan al’amuran nahiyar Afurka. Misali jaridar Die Tageszeitung ta sake nazarin hadin kan da aka samu tsakanin kungiyoyin adawa na kasar Cote d’Ivoire ya fafutukarsu na tabbatar da hadin kan kasar da kuma kawo karshen yakin basasarta. Jaridar ta ci gaba da cewar:

“Wadannan jam’iyyun hamayya guda biyu suna masu tunawa ne da tsofon shugaban kasar Cote d’Ivoire Felix Houphouet-Boigny, wanda ya rasu a shekarar 1993, a sakamakon haka suka ba wa hadin kan nasu taken: Gamayyar magoya bayan manufofin Houpouet-Boigny dake fafutukar tabbatar da demokradiyya da kwanciyar hankali. A karkashin mulkin kama karya na Houpouet-Boigny dai, akalla, kasar Cote d’Ivoire ta kasance cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Sai dai kuma a daya bangaren wannan hadin kai da aka samu tsakanin Henri Konan Bedie da Alassane Ouattara ya zama abin mamaki ga da yawa daga al’umar kasar ganin yadda aka yi tsawon shekaru da dama jami’an siyasar biyu basa ga maciji da juna. Bugu da kari kuma a karkashin shugabancin Bedie ne aka gabatar da dokar nan ta dan kasa tsantsa dake hana tsattsan bakin da aka haife su a Cote d’Ivoire shiga zabe ko mallakar kadarori a kasar.”

Bisa ga dukkan alamu tsofon shugaban kasar Liberiya Charles Taylor na ci gaba da shirya makarkashiya iri dabam-dabam domin ta da zaune tsaye a wasu sassa na yammacin Afurka, inda ake kuma zarginsa da ma’amalla da kungiyar Al-Ka’ida. A lokacin da take gabatar da rahoto akan haka jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

“Bincike ya nuna cewar a lokacin da Charles Taylor ya tashi daga Liberiya domin neman mafaka a Nijeriya ya kasance yana da zunzurutun kudin da ya kai dalar Amurka miliyan 150 zuwa miliyan 210. Kuma tun daga sannan kudade ke ci gaba da kwarara zuwa baitul-malinsa daga sassa dabam-dabam abin da ya hada har da ita kanta Liberiya. Domin kuwa tsofon shugaban ne ke mallakar kamfanin sadarwa daya kwal a Liberiya, kuma an gano cewar yana da ajiya a bankuna a kasashen Ghana da Burkina Faso da Cote d’Ivoire da Faransa da Italiya da Liechtenstein da Switzerland da Panama da sauran kasashe na yankin Karibiya. A dai halin da ake ciki yanzun kasashe da dama na dada yin matsin lamba akan shugaba Olusegun Obasanjo domin ya tasa keyarsa zuwa kotun kasa-da-kasa dake cin shari’ar masu miyagun laifuka na ta’asar yaki a Saliyo.”

A wani taron kasashe masu ba da lamunin da aka gudanar a Habasha an cimma daidaituwa akan taimaka wa rundunar kiyaye zaman lafiya da kungiyar tarayyar Afurka zata tsugunar a lardin Darfur da zunzurutun kudi na dala miliyan 200. Jaridar Süddeutsche Zeitung ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

“Wannan taimako, kamar yadda aka ji daga bakin sakatare-janar na MDD Kofi Annan, yana da muhimmanci matuka ainun kuma ba saboda kiyaye zaman lafiya kadai ba, kazalika domin ba wa mazauna lardin Darfur cikakkiyar dama ta noma gonakinsu ta yadda ba za a fuskanci karancin abinci nan gaba ba. Kimanin sojojin kinyaye zaman lafiya dubu 7 da 700 kungiyar tarayyar Afurka ke da niyya tsugunarwa a lardin.”

A cikin wata sabuwa kuma a can kasar Zimbabwe an tsare ‘yan tireda kusan dubu 10 a cikin kwanaki biyar kacal, a karkashin wani matakin da gwamnatin shugaba Mugabe ta dauka na murkushe ‘yan tireda da ake zarginsu da laifin tsawwala farashin kaya. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung ci gaba tayi da cewar:

“Tun bayan tabarbarewar cinikin ketare na kasar Zimbabwe mutane suka dogara kacokam akan saye da sayarwa domin samun kudaden shiga. Kusan kashi daya bisa hudu na al’umar Zimbabwe su miliyan 16, suka juya wa kasar baya sannan daga cikin wadanda suka rage kuma kashi 80% ba su da aikin yi, a yayinda a daya hannun darajar takardun kudin kasar ke dada faduwa, lamarin dake haddasa hauhawar farashin kaya ba kakkautawa.”