1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

May 20, 2005

Daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus akan aL#amuran Afurka a wannan makon har da zaben majalisar dokokin kasar Habasha da aka gudanar ranar lahadi da ta wuce

https://p.dw.com/p/BvpG
Shugaba Obasanjo na Nijeriya da tsofon shugaban Liberiya Charles Taylor
Shugaba Obasanjo na Nijeriya da tsofon shugaban Liberiya Charles TaylorHoto: AP

A wannan makon jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni da dama akan nahiyar Afurka, kama daga halin da ake ciki a kasar togo zuwa ga hadin guiwar da aka samu tsakanin ‘yan adawa a kasar Cote d’Ivoire da kuma yadda tsofon shugaban Liberiya Charles Taylor, har yau yake da hannu dumu-dumu a kashe-kashen gillar da ake fuskanta a kasar. Amma da farko zamu duba rahoton jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta a game da zaben kasar Habasha da aka gudanar ranar lahadi da ta wuce. Jaridar ta ce:

“’Yan hamayya na kasar Habasha sun zargi gwamnatin P/M Meles Zenawi ta aikata magudi a zaben majalisar dokokin kasar da aka gudanar ranar lahadi da ta wuce. Domin mayar da martani akan wannan zargi, nan take gwamnati ta kafa dokar haramta taron jama’a har tsawon wata daya sannan ta sanya jami’an tsaro a cikin shirin ko ta kwana. Shugaban hukumar zabe Kamal Badri, a nasa bangaren ya zargi ‘yan hamayyar da garaje wajen kalubalantar sakamakon zaben tun kafin a gabatar da shi. Wannan dai shi ne karo na uku da aka gudanar da zaben majalisar dokokin a cikin tarihin kasar Habasha na sama da shekaru dubu uku.”

Rahotanni masu nasaba da kungiyoyin kare hakkin dan-Adam sun nuna cewar mutane kimanin 800 ne suka yi asarar rayukansu sakamakon rikicin baya-bayan nan a kasar Togo. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

“Bisa ga dukkan alamu barnar da aka fuskanta dangane da sakamakon zaben shugaban kasar Togo da ake sabani kansa ta zarce yadda ake zato. A cikin wani rahoton da kungiyar kare hakkin dan-Adam ta kasar ta bayar tayi nuni da cewar mutane kimanin 790 suka mutu sannan wasu sama da dubu 4 suka ji rauni tun abin da ya kama daga lokacin da aka fara yakin neman zaben kasar a ranar 28 ga watan maris da ya wuce. Har kura ba ta lafa sosai ba. Kuma wasu alkaluma na MDD sun ce mutane sama da dubu 26 suka tsere domin neman mafaka a makobtan kasashe na Ghanada Benin.”

A wanisabon ci gaba kuma gaggan jam’iyyun hamayya na kasar Cote d’Ivoire sun cimma yarjejeniyar hadin guiwa a zaben kasar da za a gudanar watan oktoba mai zuwa. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

“A karkashin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin jam’iyyar RDR ta Allassane Ouattara da PDCI ta Henri Konan Bedie, kowace daga cikin jam’iyyun guda biyu zata tsayar da dan takararta na neman shugaban kasa a zagayen farko na zaben, sannan idan an shiga zagaye na biyu daya zai janye domin ba da goyan baya ga dan takarar dake da cikakkiyar alama ta samun galaba. Wannan hadin guiwar dai tana da ban mamaki, domin kuwa a matsayinsa na shugaban kasa Henri Konan Bedie yayi amfani da dokar dan kasa tsantsa domin hana Ouattara shiga takarar zaben shugaban kasa, wai saboda iyayensa ‘yan usulin Burkina Faso ne.”

Ana zargin tsofonshugaban kasar Liberiya Charles Taylor da shirya makarkashiyar kashe-kashe na gilla da tayar da zaune tsaye a kasar Liberiyar da kasashen dake makobtaka da ita, inda aka ce yana da hannu dumu-dumu a yunkurin kisan gillar da aka yi akan shugaban kasar Guinea Lasana Konte a cikin watan janairun da ya wuce. Jaridar Süddeutsche Zeitung dake ba da wannan rahoto ta ce da wannan yunkuri yayi nasara da ke nan an sake bude wani sabon babi na rikici a yammacin Afurka. Jaridar sai ta kara da cewar:

“A sakamakon mummunar rawar da Taylor ke takawa na neman ta da zaune tsaye a shiyyar yammacin Afurka baki daya kasashe ke dada yin matsin lamba akan shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo da ya tasa keyar Taylor domin fuskantar shari’a a kotun kasa da kasa dake da laifukan ta’asar yakin Saliyo. Akwai masu kyautata zaton cewar mai yiwuwa a wayi gari Taylor ya bi dare ya tsere daga Nijeriya tun kafin kasar tayi yunkurin danka shi ga hannun kotun ta kasa da kasa a Saliyo.”