1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

April 15, 2005

Zazzabin Marburg dake addabar kasar Angola na daya daga cikin matsalolin da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus a game da nahiyar Afurka

https://p.dw.com/p/BvpL

A wannan makon muhimman batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus dangane da al’amuran nahiyar Afurka sun hada da halin da fursinonin siyasa ke ciki a Equatorial Guinea da kokarin sasanta rikicin Cote d’Ivoire da ci gaban da ake samu dangane da rikicin Kongo sai kuma cutar nan ta Marburg dake addabar kasar Angola.

A wannan makon sojan kiyaye zaman lafiya na MDD sun tashi haikan a kokarinsu na murkushe baraden sa kai dake kashe-kashe na ba-gaira a gabacin kasar Kongo. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG cewa tayi:

"Ba zato ba tsammani an fara samun haske a game da rikicin kasar Kongo. Domin kuwa a ‘yan makonnin baya-bayan nan an fara samun wani ci gaba da ba a taba ganin irin shigensa ba a gabacin Kongo, inda ‘yan ta kife ke kashe-kashe na ba-gaira akan talakawan yankin. Kusan a kowace rana ta Allah sai sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD sun ba da sanarwa akan wasu nasarori da suka cimma akan manufa. Kimanin kashi biyu bisa uku na dakarun sa kai a lardin Ituri suka mika makamansu, sannan aka cafke shugabannin ‘yan tawaye da da masu laifukan ta’asar yaki. Wannan ci gaba ya zo ne sakamakon sa baki da kwamitin sulhu na MDD yayi wajen ganin sojan kiyaye zaman lafiyar sun tashi tsaye domin murkushe ‘yan ta kifen dake cin karensu ba babbaka a wannan yanki."

A kokarin da yake na sasanta rikicin kasar Cote d’Ivoire da sunan kungiyar tarayyar Afurka, shugaba Thabo Mbeki na Afurka ta Kudu ya ba da shawarar yin kwaskwarima ga daftarin tsarin mulkin kasar domin ba wa jami’in hamayya Alassane Quattara damar tsayawa zaben kasar da aka shirya gudanarwa a cikin watan oktoba mai zuwa. A lokacin da take ba da rahoto game da haka jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

"A matsayinsa na mai shiga tsakani domin sasantawa shugaba Thabo Mbeki na ATK ya tsayar da shawarar cewa wajibi ne dukkan masu hannu a shawarwarin sasanta rikicin kasar Cote d’Ivoire su samu cikakkiyar dama ta shiga zaben kasar da aka shirya gudanarwa a cikin watan oktoba mai zuwa. Wannan matsalar kuwa ita ce ainifin musabbabin rikicin da ya kai ga yakin basasa a wannan kasa ta yammacin Afurka, wacce a karkashin daftarin tsarin mulkinta dake cewar wai duk wani mai neman zama shugaban kasa wajibi ne ya zama cikakken dan kasar Cote d’Ivoire tsantsa."

A wannan makon kungiyar neman afuwa ta Amnesty International tayi kakkausan suka a game da halin da fursinoni ke ciki a gidajen kurkuku na kasar Equatorial Guinea, inda aka ce akalla fursinoni 70 ke fuskantar barazanar mutuwa sakamakon radadin yunwa. Jaridar Frankfurter Rundschau ta gabatar da rahoto akan haka inda take cewar:

"Kimanin fursinoni saba’in, a tsakaninsu har da ‘yan kasashen waje su 11, suke fama da mawuyacin hali a gidan kurkukun Black-Beach dake Malabo, fadar mulkin kasar Equatorial Guinea mai arzikin man fetur. Fursinonin, wadanda akasarinsu fursinonin siyasa ne, sun kamu da cututtuka kuma wasu daga cikinsu na fama da maganin mutuwa sakamakon azabtarwa daga hannun mahukuntan yarin. Matakan azabtarwar, kamar yadda aka ji daga kungiyar Amnesty sun hada da kin ba wa fursinonin abinci ko kula da lafiyarsu, lamarin da ta ce abin kunya ne ga mahukuntan wannan kasa mai yawan al’uma dubu 500 kacal."

Sama da mutane 213 zazzabin nan na Marburg ya kashe a kasar Angola kuma tuni cutar ta dauki wani salo na annobar dake neman yaduwa zuwa sauran sassa na Angola, abin da ya hada har da fadar mulki ta Luanda mai yawan mazauna miliyan hudu da kuma babban filin jiragen sama. A sakamakon haka kasashe da dama dake da dangantakar zirga-zirgar jiragen sama tsakaninsu da Angola, kamar Afurka ta Kudu da Brazil da kuma Portugal suka fara daukar matakan binciken lafiyar duk wani fasinja da ya sauka daga Angola domin tabbatar da cewar ba ya dauke da wannan zazzabi mai yaduwa tsakanin jama’a. Wannan rahoton jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ce ta gabatar da shi.