1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

April 1, 2005

Zaben kasar Zimbabwe shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan makon

https://p.dw.com/p/BvpM

A wannan makon dai, kamar yadda aka tsammata tun farko, jaridu da mujallun Jamus sun fi mayar da hankalinsu ne akan kasar Zimbabwe, dangane da zaben majalisar dokokin kasar da aka gudanar a jiya alhamis. Jaridu da mujallun na Jamus sun yi amfani da wannan dama domin gabatar da sharhi akan halin da kasar take ciki yanzun. A cikin nata sharhin jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG cewa tayi:

"Yau tsawon shekaru 25 ke nan da Robert Mugabe ke shugabancin kasar Zimbabwe, wacce a zamanin baya ta zama tamkar rumbun hatsin Afurka. Amma tun bayan da dan kama karyar ya fara daukar matakan fatattakar manoma farar fata da kuma kwace gonakinsu domin raba wa ‘yan bangansa, kuma tun daga sannan al’amuran Zimbabwe suka shiga tabarbarewa sannu a hankali. Jama’a na fama da yunwa sannan tattalin arzikinta na fuskantar mummunan koma baya. Amma duk da haka Mugabe na kan bakansa na ci gaba da mulkar kasar ko ta halin kaka. Hatta zaben majalisar dokokin da aka gudanar a jiya alhamis ba zai kawo wani canji ba."

Ita kuwa Mujallar FOCUS ta yi amfani da wannan dama ne domin nazarin halin da manoma farar fata da Mugabe ya kora suke ciki a inda suka samu mafaka a kasar Zambiya. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Kasar Zambiya sai murna da doki take yi tare da fatan cewar Mugabe zai dore akan karagar mulkin kasarsa ta Zimbabwe. Domin kuwa manoma farar fatar da ya kora, ita kuma a nata bangaren ta karbi bakuncinsu tana mai raba musu filayen noma, suna taimakawa wajen bunkasar kasar matuka da aniya. Babban misali shi ne ganyen taba, wanda a zamanin baya yake samarwa da kasar zimbabwe kudaden musaya na ketare, a yanzu sai dada bunkasa yake yi a kasar Zambiya, inda a cikin shekaru hudu kacal yawan abin da kasar ke nomawa ya tashi daga tan dubu biyar zuwa tan dubu talatin. Bugu da kari kuma a karon farko a cikin tarihinta, kasar ta Zambiya, a wannan shekarar zata samu rarar hatsi da take nomawa. Kazalika nan ba da dadewa ba kasar zata fara fitar da masara zuwa ketare, bayan shekaru da dama da tayi tana mai dogara akan taimakon abinci daga kafofi na kasa da kasa. Ta la’akari da haka bai zama abin mamaki ba ganin yadda kasashe kamarsu Nijeriya da Uganda da makamantansu suka rika yi wa farar fatar da Zimbabwe ta kora tayin filayen noma."

A wannan makon MDD ta gabatar da wasu matakai na takunkumi akan mutanen da ake zariginsu da alhakin keta haddin dan-Adam a lardin Darfur, bayan da kasar Amurka ta janye daga adawar da tayi da wannan manufa da farko. Jaridar NEUES DEUTSCHLAND ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

"Wannan takunkumin, wanda ya tanadi haramcin tafiye-tafiye da kuma dora hannu akan kadarorin masu laifukan ta’asar keta haddin dan-Adam a lardin Darfur na yammacin Sudan, yana da nufin karya alkadarin wasu masu taurin kai ne dake hana ruwa gudu wajen samar da zaman lafiya a Darfur tare da barazanar ci gaba da ta da zaune tsaye a wannan yanki. A makon jiya ne dai kwamitin sulhu na MDD ya tsayar da kudurin tura dakarun kiyaye zaman lafiya dubu 10 zuwa Sudan domin sa ido akan yarejeniyar zaman lafiyar kudancin kasar a cikin watan janairun da ya wuce."

A cikin wata sabuwa kuma ‘yan tawayen Hutu sun bayyana shirinsu na dakatar da fada akan Ruwanda. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ce ta gabatar da wannan rahoton ta kuma ci gaba da cewar:

"Ba zato ba tsammani ‘yan tawayen Hutu sun fito fili suna Allah Waddai da kisan kiyashin da ya wanzu a kasar Ruwanda shekaru 11 da suka wuce, sannan suka bayyana shirinsu na dakatar da fada akan gwamnatin kasar. Wannan shawarar na da nufin ba da gudummuwarsu ne a kokarin kawo karshen rikicin Ruwanda da ya ki ci ya ki cinyewa."