1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

March 4, 2005

Halin da ake ciki a kasar Kongo shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan makon

https://p.dw.com/p/BvpQ

A wannan makon jaridun na Jamus sun mayar da hankalinsu ne akan halin da ake ciki a kasashen Somaliya da Kongo da kuma Togo. A lokacin da take ba da rahoto game da kasar Somaliya, mujallar DER SPIEGEL mai fita mako-mako cewa tayi:

"Kusan babu wata kasa a doron duniyar nan tamu da ta gagari mulki kamar kasar Somaliya, wacce tun misalin shekaru 14 da suka wuce bata da wata tsayayyar gwamnati. Amma fa duk da haka, abin mamaki, al’amura na tafiya salin alin a wasu bangarori na birnin Mogadishu. Kasar na da tashoshin telebijin guda 15 da kuma kamfanonin tarfo ta salula guda 20. A cikin watan yunin bara kamfanonin Coca Cola ya bude reshensa a can, a yayinda da yawa daga gaggan kamfanoni na kasa da kasa suke bakin kokarinsu na neman hakkin hakar mai a kasar dake fama da yamutsi, wacce kuma hanyoyinta na kiwon lafiya suka dara na wasu kasashen Afurka dake da zaman lafiya."

A sakamakon kisan gillar da aka yi wa sojan kiyaye zaman lafiya na MDD a kasar Kongo, a yanzun akwai barazanar tabarbarewar matakin kiyaye zaman lafiyar, wanda shi ne mafi girma irinsa da MDD ta dauka. Jaridar DIE TAGESZEITUNG ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

"MDD ta shiga wani mawuyacin hali na kaka-nika-yi dangane da ayyukanta na kiyaye zaman lafiya a kasar Kongo sakamakon kisan gillar da aka yi wa wasu sojojinta guda tara a ranar juma’ar da ta gabata. Akwai yiwuwar janye dukkan masu alhakin matakan na kiyaye zaman lafiya, musamman ma ganin zargin da ake wa sojojin na cin mutuncin mata da kuma rashin tabuka kome domin dakatar da ta’asar ‘yan takife dake cin karensu ba babbaka a gabacin kasar Kongo. A halin yanzu haka akwai masu batu a game da tsunduma kasar cikin yamutsi irin shigen na kasar Somaliya, inda a shekarar 1993 sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa suka janye sakamakon hare-haren da suka rika fuskanta daga daga wasu dakarun sa kai."

A nata bangaren jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG tayi bitar halin da ake ciki a kasar ta Kongo ne tare da ba da la’akari da wani matakin farmaki da sojan kiyaye zaman lafiya na MDD suka dauka akan dakarun sa kai domin mayar da martani. Sai dai kuma ta ce har yau al’umar kasar na kyamar sojojin na kiyaye zaman lafiya. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Duk da matakin nuna karfin hatsi da sojan kiyaye zaman lafiya na MDD suka dauka a tsakiyar wannan makon domin dawo da martabarsu da ta zube a idanun jama’a, amma fa har yau al’umar Kongo na kyamar sojojin kiyaye zaman lafiyar, wadanda a ganinsu sun zo yawon shakatawa ne kawai amma ba su da ikon tabuka kome. Dalili kuwa shi ne sun dade suna fama da ta’asar ‘yan takife, a yayinda sojojin ke zura ido suna kallo, a baya ga zargin da ake musu na cin mutuncin mata a wannan kasa."

Ba zato ba tsammani sabon shugaban kasar Togo Faure Eyadema ya ba da kai bori ya hau ga matsin lamba ta kasa da kasa domin yayi murabus. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

"An yi marhabin da wannan mataki da Faure Eyadema ya dauka domin yin murabus da ba wa sabon kakakin majalisar dokokin kasar da aka nada a karshen mako Abbas Bonfoh damar tafiyar da al’amuran mulkin kasar ta yammacin Afurka har ya zuwa zaben shugaban kasar da za a gudanar a cikin kwanaki sittin masu zuwa, kamar yadda daftarin tsarin mulkinta ya tanada. To sai dai kuma har yau da ayar tambaya a game da ko shin wannan murabus zai ba da wata kyakkyawar dama ta gudanar da zabe tsakani da Allah. Domin kuwa shi kansa sabon kakakin majalisar dokokin ya kasance daya daga na gaban goshin marigayi Gnassingbe Eyadema kuma sai da sa baki wajen aiwatar da kwaskwarima ga daftarin tsarin mulkin kasar ta Togo domin ba wa Faure damar kama madafun mulki."