1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

February 11, 2005

Halin da ake ciki a kasar Togo shi ne masharhanta na jaridun Jamus suka mayar da hankali kansa a wannan makon

https://p.dw.com/p/BvpT

Muhimmin abin da ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a game da al’amuran nahiyarmu ta Afurka shi ne halin da ake ciki a kasar Togo bayan mutuwar shugaba Eyadema da kuma gadon karagar mulkin da dansa yayi. A lokacin da take gabatar da rahoto akan haka jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

"Mutuwar shugaba Eyadema ke da wuya, sai majalisar dokokin kasar Togo tayi wa daftarin tsarin mulkin kasar gyaran fuska domin ba wa dansa ikon mayewa gurbinsa bayan da sojoji suka hana wa kakakin majalisar dokokin dake ziyara a ketare damar komawa gida domin ci gaba da mulkin rikon kwarya kafin a shirya wani sahihin zabe na demokradiyya. A yanzun dai ba wanda ya san yadda al’amura zasu kaya a game da makomar siyasar kasar ta yammacin Afurka, inda ‘yan hamayya suka tubre cewar zasu shiga gwagwarmaya har sai sun ga bayan wannan haramtacciyar gwamnati da aka nada."

Ita kuwa jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG tayi nuni ne da matsaloli na kabilanci dake addabar manufofin siyasar kasashen yammacin Afurka, lamarin dake dada durmuyar da kasashen yankin a cikin mawuyacin hali na yake-yaken basasa. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Ga alamu dai kaddarar da ta rutsa da kasashen Liberiya da Saliyo da kuma Cote d’Ivoire sakamakon kabilanci, ita ce ke barazanar rutsawa da kasar Togo yanzu haka, saboda mulkin marigayi Eyadema ya dogara ne kacokam akan siyasar kabilanci. Ana iya lura da wannan barazana a lafazin da ya fito daga bakin shugaban ‘yan hamayyar kasar ta Togo Gilchrist Olympio, wanda ya lashi takobin daura damarar yaki muddin ba a share hanyar gudanar da sahihin zabe na demokradiyya ba."

A can lardin Darfur na kasar Sudan, ko da yake bayanai na MDD sun ce ba a aiwatar da danyyen aiki na kisan kare-dangi ba, amma fa har yau ana ci gaba da zub da jini a cewar jaridar DER TAGESSPIEGEL. Jaridar sai ta kara da cewar:

"Tun bayan fara yakin lardin Darfur misalin shekaru biyu da suka wuce an halaka mutane sama da dubu 70 a yayinda wasu miliyan daya da dubu dari takwas ke kan gudun hijira. Taron sulhun da aka gabatar a Abujan Nijeriya ya tarwatse ba tare da an kai ga tudun dafawa ba a wajejen tsakiyar watan desamban da ya gabata. Kungiyoyi na ‘yan tawayen dai suna dada samun karin dakarun sa kai, ko da yake akasarinsu yara ne wadanda da kyar suka samu shekaru 16 da haifuwa."