1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

February 4, 2005

Halin da ake ciki a lardin Darfur shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan makon

https://p.dw.com/p/BvpU

A wannan makon jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni da dama akan al’amuran nahiyarmu ta Afurka, ko da yake sun fi mayar da hankali ne ga halin da ake ciki a lardin Darfur na kasar Sudan. Amma da farko zamu fara ne da rahoton mujallar mako-mako ta DER SPIEGEL wacce ke tunasarwa da yakin kasar Kongo da duniya tayi ko oho da shi. Mujallar sai ta ci gaba da cewar:

"Sama da mutane miliyan uku suka yi asarar rayukansu a can kafon zuciyar nahiyar Afurka, wato kasar Kongo, a ‘yan shekarun baya-bayan nan ba tare da duniya ta dauki wani nagartaccen mataki na katsalandan ba. A kuma halin da ake ciki yanzun rikicin na iya sake barkewa saboda kokarin da Ruwanda take yi na hana wanzuwar zaben da aka shirya gudanarwa a kasar ta Kongo nan gaba a wannan shekara, inda take zuga sassan da basa ga maciji da juna domin kara rura wutar sabanin dake tsakaninsu. Babban dalilin take-taken Ruwandan kuwa shi ne tsabar kwadayin albarkatun kasar da Allah Ya fuwace wa Kongo."

A wannan makon hukumar kwamitin sulhu na MDD akan al’amuran Darfur ta kakkabe gwamnatin Sudan daga zargin ta’asar kisan kare-dangin da ake mata ko da yake ta hakikance cewar dukkan dakarun sa kai na Janjaweed da sojojin gwamnati dake rufa musu baya sun caba miyagun laifuka. Jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

"Bayan bin bahasi na tsawon watanni uku da tayi hukumar MDD akan al’amuran Darfur ta gano cewar gwamnatin Sudan da dakarun sa kai na Janjaweed na da alhakin miyagun laifuka na keta haddin dan-Adam. Dakarun Janjaweed da sojojin gwamnati sun kai hare-hare akan farar fula suna masu kashe-kashe na gilla da fatattakar mutane daga yankunansu na asali da bannatar da kauyuka ba gaira ba dalili. Bisa ga dukkan alamu kuwa wannan matakin wani bangare ne na siyasar fadar mulkin Khartoum a kokarinta na karya alkadarin ‘yan tawaye. Hukumar ta kwamitin sulhu ta gabatar da sunayen wasu jami’an Sudan da take gani wajibi ne a gurfanar da su gaban ktotun kasa-da-kasa domin amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa."

Ita kuwa jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG tayi nuni ne da cewar ko da yake ba a samu fadar mulkin Sudan da laifin kisan kare-dangi ba, amma duk da haka bai kamata a zauna a harde kafafuwa tare da sa mata ido tana cin karenta babu babbaka ba.

Bisa ga dukkan alamu yake-yaken basasa a nahiyar Afurka sun kai wa Kungiyar Tarayyar Afurka iya wuya, kuma har yau tana ci gaba ne da lalube a cikin dufu wajen neman bakin zaren warware rikice-rikice guda uku da suka zame mata kayar kifi a wuya. Wadannan rikice-rikice sun hada da na Cote d’Ivoire da Kongo da kuma Sudan. Wannan bayanin, jaridar DIE TAGESZEITUNG ce ta gabatar da shi bayan wani nazari da tayi, inda ta ci gaba da cewar:

"Rikice-rikicen kasashen Kongo da Cote d’Ivoire da Sudan duk jirgi daya ke dauke da su, wato bi ma’ana rikice-rikice ne da suka fi karfin Kungiyar Tarayyar Afurka, amma kuma a daya hannun ba za a iya warware wadannan rikice-rikice ba sai tare da taimakon kungiyar. A dai halin da ake ciki yanzun abin da zai taimaka shi ne a samu kakkarfan hadin kai tsakanin Kungiyar ta Tarayyar Afurka da MDD. A yayinda ita kungiyar AU zata mayar da hankali wajen sasantawa ita kuma MDD ka iya daukar matakai na takunkumi jan kunnen masu nuna taurin kai da hana ruwa gudu wajen cimma sulhu."