1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

January 21, 2005

Halin da ake ciki a kasar Sudan na daga cikin abubuwan da jaridu da mujallun Jamus suka yi sharhi akansa a wannan makon

https://p.dw.com/p/BvpW

Halin da ake ciki a kasar Sudan bayan yarjejeniyar sulhu da aka kulla tsakanin shugaba El-Bashir da madugun ‘yan tawaye John Garang na daya daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin da jaridu da mujallun Jamus suka bayar a wannan makon mai karewa. A cikin nata rahoton mujallar DER SPIEGEL tayi nuni ne da cewar bayan wannan yarjejeniya ta sulhu da aka kulla a yanzun kasar Sudan na fuskantar barazanar fadawa cikin wani sabon rikicin dangane da gwagwarmayar da kamfanonin mai na kasashen Amurka da China ke yi domin cin gajiyar arzikin mai da Allah Ya fuwace wa wannan kasa. Mujallar sai ta ci gaba da cewar:

"Ita dai Amurka ta dade tana mai taka muhimmiyar rawa wajen neman bakin zaren warware rikicin kasar Sudan tana mai yin tasiri akan kristoci masu zazzafan ra’ayi a kudancin kasar, wadanda suka mayar da yakin basasar tamkar wani rikici na addini. To sai dai kuma Amurkan tayi hakan ne saboda tsabar son kai. Domin kuwa kimanin kashi 60 na man da Sudan ke haka ana jigilarsa ne zuwa kasar China, sakamakon takunkumin da Amurka ta kakaba wa kamfanonin kasar game da zuba jari a Sudan. Amma a yanzun za a soke wannan takunkumi bayan yarjejeniyar ta sulhu. Dangane da haka manazarta ke hangen wani yanayi na gwagwarmayar dora hannu akan rijiyoyin man Sudan tsakanin Amurka da China, musamman ma ganin cewar Amurka na fatan dogara akan nahiyar Afurka wajen nemo kashi ¼ na yawan mai da take saya daga ketare."

Babbar matsalar dake hana ruwa gudu dangane da sasanta rikicin kasar Kongo shi ne zaben da aka shirya gudanarwa a kasar a cikin watan yuni mai zuwa, amma ake fuskantar matsalolin da ka hana ruwa gudu bisa manufa. A cikin rahoton da ta bayar jaridar DIE TAGESZEITUNG ta ce zai zama abin mamaki idan har an samu kafar gudanar da wannan zaben ma a karshen shekarar nan da muke ciki. Jaridar ta bayyana wasu daga cikin dalilan haka, inda take cewar:

"Ayyukan gwamnati sun gurgunce baki daya kuma an shiga wani sabon hali na zaman doya da manja tsakanin shugaba Joseph Kabila da mataimakinsa, madugun ‘yan tawayen kungiyar MLC Jean-Pierre Bemba, wanda ya bijire wa gwamnati domin matsin lambar ganin lalle sai an sake shigar da wani dan gaban goshinsa mai suna Endundu a majalisar ministocin shugaba Kabila, bayan gusar da shi da aka yi sakamakon laifin cin hanci. MLC tayi barazanar ficewa daga gwamnatin hadin gambizan baki daya nan da karshen watan janairu. Hakan zai kara gurgunta gwamnatin, wacce tuni dama take cikin kaka-nika-yi sakamakon bijirewar daya kungiyar tawayen ta RDC mai angizo a gabacin Kongo, a wajejen tsakiyar shekarar da ta wuce."

A cikin wata sabuwa kuma a wannan makon an samu rahoton wani yunkuri na juyin mulki a kasar Guinea. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

"Babu dai wani cikakken bayani a game da wannan yunkuri na juyin mulki. Amma a daya bangaren ainifin abin da ya faru yana mai yin nuni ne da irin hali na zaman dardar da ake ciki a kasar Guinea ta yammacin Afurka, wacce ake fargaba ka da kaddara ta rutsa da ita daidai da makobtanta irinsu Liberiya da Saliyo ta fada cikin wani yaki na basasa. Al’umar kasar na cikin mawuyacin hali na rayuwa sannan ita kuma gwamnati tana ci gaba da danne ‘yan hamayya. Wani abin lura ma shi ne kasancewar Guinea na daya daga cikin kasashen da suka fi fama da talauci a duniya duk kuwa da dimbim albarkatun kasa da Allah Ya fuwace mata."