1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

October 1, 2004

Rikicin yankin Niger-Delta a Nijeriya shi ne muhimmin abin da ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon mai karewa

https://p.dw.com/p/Bvpg

A wannan makon mai karewa dai muhimmin abin da ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus shi ne ta da kayar baya da wasu dakarun sa kai suka yi a yankin Niger-Delta na Nijeriya suna masu haddasa rudami da rashin sanin tabbas a kasuwannin mai na kasa da kasa. A lokacin da take gabatar da sharhi akan haka jaridar DIE TAGESZEITUNG nuni tayi da cewar:

"A daidai yau juma’a ne kasar Nijeriya, wacce ita ce ta bakwai a tsakanin kasashen da suka fi cinikin mai a duniya kuma ta biyar a tsakanin kasashen kungiyar OPEC dake da arzikin man fetur, take bikin samun shekaru 44 ga ‘yancin kanta, amma fa murna na neman komawa ciki domin kuwa daidai wannan ranar ce kuma wasu dakarun sa kai a yankin Delta suka ware domin gabatar da abin da suka kira wai yakin neman adalci akan kwarar al’umar Ijaw da ake yi wajen rabon ribar da Nijeriya take samu daga man da ake hakowa daga yankinsu. Wannan mataki da dakarun sa kan su kimanin dubu biyu suka dauka a karkashin madugunsu mai suna Alhaji Dokubo Asari, tsofon shugaban dalibai mai zazzafan ra’ayi da ya rungumi musulunci, ya haifar da rudami da rashin sanin tabbas a kasuwar hada-hadar mai ta kasa-da-kasa. Rikicin na yankin Delta yayi sanadiyyar rayukan mutane sama da 500 a cewar kungiyar afuwa ta Amnesty International."

Ita ma jaridar NEUES DEUTSCHLAND mai ra’ayin gurguzu ta yi bitar abin da ta kira yakin dakarun sa kai akan gwamnatin Nijeriya da kamfanonin mai dake gudanar da ayyukansu a kasar. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Wata kungiya ta ‘yan tawaye dake kiran kanta wai: Kungiyar dakarun sa kai ta al’umar Deltan nijeriya, ta lashi takobin gabatar da yakin da ba a taba ganin irin shigensa ba a wannan kasa tun daga ranar daya ga watan oktoba. Kungiyar ta ce lalle sai kamfanonin mai na ketare su tattara nasu ya nasu su fice daga yankin bisa zarginsu da laifin rufa wa gwamnati baya a matakinta na kisan kiyashin da aka yi wa mazauna yankin Delta. Wani mai magana da yawun kamfanin agip ya ce kamfanin zai ci gaba da aikinsa ba kakkautawa kuma zargin na kisan kare dangi kage ne kawai, wanda ba ya da tushe."

A wannan makon ministan cikin gida na Jamus ya sake jaddada shawararsa game da gina sansanin karbar ‘yan gudun hijira na kasashen Afurka bakar fata a wata kasa ta arewacin Afurka domin hana tuttudowarsu zuwa nahiyar Turai. A lokacin da take sharhi game da haka jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG cewa tayi:

"Bisa ga ra’ayin ministan cikin gidan Jamus Otto Schily akwai bukatar daukar tsauraran matakai domin dakatar da mummunan ci gaban da ake samu a yankin tekun bahar rum inda a shekarar da ta gabata kawai mutane sama da dubu biyar suka yi asarar rayukansu a kokarin shigowa nahiyar Turai ta barauniyar hanya. To sai dai kuma wannan shawarar tasa tana fuskantar mummunan suka daga bangarori dabam-dabam na siyasar Jamus, wadanda suke ganin wannan mataki tamkar wani yunkuri ne na kakkabe nauyin da ya rataya a wuyan kasashen Turai na karbar ‘yan gudun hijira domin danka alhakin lamarin akan wasu kasashe na ketare."