1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

September 17, 2004

Ire-iren ci gaban da Kungiyar Tarayyar Afurka take samu akan manufofin da ta sa gaba na daya daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon mai karewa

https://p.dw.com/p/Bvpi

A wannan makon ko da yake jaridun Jamus sun gabatar da rahotanni a game da halin da ake ciki a yankin Darfur na kasar Sudan da kuma rikicin da aka shiga a kasar Kongo, amma duk da haka masharhanta na jaridun sun yaba da ire-iren ci gaban da ake samu wadanda ke ba da kwarin guiwa a game da makomar Afurka. Amma da farko zamu duba abin da jaridar DIE TAGESZEITUNG take cewa ne dangane da rikicin kasar Kongo, inda a wannan makon dubban mazauna gabacin kasar suka kama hanyarsu ta gudun hijira sakamakon matakan kutse da sojojin gwamnati ke dauka akan ‘yan tawaye. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Babban dalilin wannan sabon mawuyacin halin da aka shiga inda alkaluma suka kiyasce yxawan mutanen dake kan hanyarsu ta gudun hijira ya kai mutum dubu 175, shi ne matakan da sojoji masu biyayya ga gwamnati ke dauka domin karya alkadarin sojojin da suka bijire suka koma karkashin jagorancin janar Laurent Nkunda dan usulin kasar Ruwanda. Sai dai kuma su kansu sojojin dake biyayya ga gwamnati sun kunshi dakarun kungiyar Mayi-Mayi ne da suka yi tsawon shekaru da dama suna yakar tsuraru ‘yan usulin kasar Ruwanda a gabacin Kongo, kuma ta haka wannan fadan ya dauki wani salo na rikicin kabilanci."

A can Darfur, ko da yake ana fuskantar barazanar tarwatsewar shawarwarin sulhunta rikicin yankin da ya ki ci ya ki cinyewa, amma jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta yaba da rawar da Kungiyar Tarayyar Afurka ke takawa, wadda a ganinta wata alama ce ta samun canji ga al’amuran wannan kungiya. Jaridar sai ta kara da cewar:

"A kan yi wa kasashen Afurka dariya da ba’a a game da kokarinsu na samar da wani hadin kai irin shigen na kasashen Turai, ganin yadda nahiyar ta Afurka take fama da rikice-rikice iri dabam-dabam. Amma fa an samu kyakkyawan canji tun bayan rikidewar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afurka ta OAU zuwa Kungiyar Tarayyar Afurka AU a takaice misalin shekaru biyu da suka wuce. Domin kuwa a baya ga rundunar ko-ta-kwana ta kwantar da tarzoma da kungiyar ta tura domin ba da kariya ga masu sa ido akan manufofin zaman lafiyar Darfur da Burundi, kazalika kungiyar ta na da wata hukuma akan hakkin dan-Adam da kuma kwamitin sulhu irin shigen na MDD, sai kuma wata majalisar wakilai bai daya tsakanin kasashenta, wacce a jiya alhamis ta hallara a Johannesburg na ATK domin gudanar da taronta na farko. Duka-duka matsalar da ka iya hana ruwa gudu ga ayyukan Kungiyar ta Tarayyar Afurka ita ce matsalar kudi, wadda ba shakka za a sha fama da wahala wajemn shawo kanta."

Ita ma jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta lura da wannan ci gaba, inda take cewar:

"Tare da zaman farko da majalisar wakilai bai daya ta kasashen Afurka tayi a mazauninta dake birnin Johannesburg aka shiga wani sabon yayi dangane da al’amuran wannan nahiya. Domin kuwa kamar yadda kakakin majalisar ta nunar wannan shi ne karo na farko a cikin tarihi, inda kasashen Afurka ke da ikon tattaunawa akan ire-iren abubuwan dake ci musu tuwo a kwarya. Kasar ATK ce zata dauki nauyin ayyukan majalisar har tsawon shekaru biyar masu zuwa."

Kimanin mutane talatin ne suka yi cincirindo a filin saukar jiragen saman Hamburg domin zanga-zangar adawa da matakin mahukunta na komar da wasu ‘yan gudun hijira na Afurka zuwa kasashensu. Jaridar NEUES DEUTSCHLAND dake ba da wannan rahoton cewa tayi:

"Masu zanga-zangar, wadanda suka rika rarraba kasidu ga jama’a a filin saukar jiragen samman Hamburg sun yi kakkausan suka a game da tsabar kudi Euro dubu 140 da aka kashe domin hayar jirgin samar da kwashe wadannan ‘yan gudun hijira su 17 zuwa kasashensu da suka hada da Togo da Burkina Faso da Benin a maimakon a yi amfani da wadannan kudade domin kyautata jin dadin rayuwarsu a nan kasar. Amma a daya bangaren mahukunta na Jamus da Belgium da kuma Switzerland na zargin cewar miyagun mutane ne masu tayar da kayar baya. Akan yi amfani da wannan lafazin ne domin bayani a game da ‘yan gudun hijira da kan marairaice saboda tsabar fargaba wajen komar da su gida."