1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

September 3, 2004

Matsalar farin dango na daya daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon mai karewa

https://p.dw.com/p/Bvpk

A wannan makon ma dai jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da shirye-shirye da dama dangane da al’amuran nahiyar Afurka, musamman ma ganin yadda fadar mulki ta Khartoum ta sa kafa tayi fatali da wa’adin da MDD ta kayyade mata a game da lafar da kurar rikicin Lardin Darfur na kasar Sudan. A cikin nata rahoton jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

"Wa’adin da MDD ta kayyade wa gwamnatin Sudan ya kawo karshensa, amma dakarun Larabawa masu samun daurin gindin gwamnati na ci gaba da kai hare-harensu ba kakkautawa, ko da yake an samu wata ‘yar kafa ta kai wa ‘yan gudun hijirar da suka tagayyara a lardin Darfur taimakon abinci. To sai dai kuma ayar tambaya a nan shi ne ko Ya-Allah MDD zata kakaba wa fadar mulki ta Khatoum wani mataki na takunkumi dangane da kunnen uwar shegun da tayi da wa’adin da aka kayyade mata na kwance damarar ‘yan ta-kife Larabawa dake cin karensu babu babbaka a lardin Darfur."

A sassa dabam-dabam na yankin Sahel ana fama da barazanar yaduwar farin dango, wadanda ke lalata amfanin noma suke kuma awon gaba da ciyayin da aka saba kiwata dabbobi da su. Jaridar Die Tageszeitung ta gabatar da rahoto tana mai cewar:

"A dai wannan halin da ake ciki yanzun ba wanda zai iya yin hasashen iyakacin barnar da farin dangon suka yi. Amma a hakika sun haddasa mummunar asarar amfanin noma, ko da yake ba a zaton barnar zata kai shigen wacce ta wanzu a shekarar 1988. A wancan lokaci farin sun lalata abin da ya kai kadada miliyan daya na filayen noma da wuraren kiwon dabbobi a kasar Nijer kadai, lamarin da ya kusa ya jefa kasar cikin mawuyacin hali na karancin abinci."

A kasar Equatorialguinea an samu canjin al’amura tun bayan da aka gano arzikin man fetur a cikinta a farkon shekarun 1990 ta kuma wayi gari a matsayi na hudu a tsakanin kasashen Afurka dake fitar da mai zuwa ketare. To sai dai kuma kamar yadda bayanai suka nunar kimanin kashi 80% na ribar da kasar ke samu daga cinikin man nata suna kwarara ne zuwa aljifun shugabanta dan kama-karya Teodoro Obiang da mukarrabansa a yayinda talakawan kasar ke cikin hali na kaka-nika-yi. A lokacin da take gabatar da rahoto a game da shugaban na Equatorialguinea, mujallar Der Spiegel cewa tayi:

"Daga baya-bayan nan an shiga ka ce na ce dangane da shugaba Obiang, abin da ya hada har da dan tsofuwar P/M Birtaniya Magreth Thatcher. An tsare shi a Capetown ta kasar Afurka ta kudu bisa zarginsa da hannu a yunkurin juyin mulkin da aka ce an gabatar akan shugaba Obiang. Tun a cikin watan maris da ya wuce ne aka yi ikirarin fallasa wannan makarkashiya ta juyin mulki, inda aka cafke wasu bakin dake aiki a Equatorialguinea abin da ya hada har da wani Bajamushen dake wa wani kamfanin Jamus daga garin Offenbach aiki a Malabo, fadar mulkin wannan kasa. Kawo yanzu kuwa ba wanda ya san yadda wannan takaddama zata kaya."

A cikin wata sabuwa kuma a halin yanzu ana fuskantar matakin rushe jam’iyyar nan ta NP ko kuma NNP, wacce ta mulki Afurka ta Kudu daga 1948 zuwa 1994 a karkashin manufofinta na wariyar jinsi. A cikin rahoton da ta bayar game da haka jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Tun da farkon fari ne ake kyautata zaton cewar jam’iyyar ta NP, wacce aka sauya mata suna zuwa NNP, ba zata yi karko ba, inda a baya-bayan nan shugabanta ya fito fili ya bayyana shirinsa na komawa inuwar jam’iyyar ANC dake mulki, kuma a wannan makon wasu gaggan jami’an jam’iyyar NNP su 23 suka canza sheka domin komawa inuwar ANC. Wannan damar da ANC ke bayarwa na karbar shuagabannin jam’iyyar NNP karkashin tutarta na da nufin bayyanarwa a fili ne cewar ita jam’iyya ce ta kowa-da-kowa amma bata da nasaba da kokarin mayar da ATK karkashin tsarin mulkin jam’iyyar siyasa daya kwal.