1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

July 9, 2004

Halin da ake ciki a Sudan da Ruwanda da kuma Kudancin Afurka shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridu da mujallun Jamus a wannan makon

https://p.dw.com/p/Bvpq

Halin da ake ciki a kasashen Sudan da Ruwanda da kuma kudancin Afurka shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus wannan makon mai karewa. Amma da farko zamu fara da wani rahoton da jaridar Süddeutsche Zeitung ta bayar a game da zanga-zangar kyamar salon mulkin shugaba Mwai Kibaki na kasar Kenya da aka gudanar a Nairobi a karshen makon da ya gabata, inda ‘yan sanda suka yi amfani da kulake da barkonon tsofuwa domin tarwatsa masu jerin gwanon. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Tun bayan mummunan hatsarin mota da kuma cutar hauhawar jini da ya fuskanta shugaba Mwai Kibaki ba ya da ikon tabuka kome, saboda galibi ma in ya fito bainar jama’a zaka tarar ba ya cikin hayyacinsa sosai saboda radadin da yake fama da shi. A sakamakon haka ministocinsa ke cin karensu babu babbaka, a maimakon su dauki sahihan matakai na garambawul da zasu taimaka wajen ta da komadar tattalin arzikin Kenya. Babu wani ci gaban da aka samu illa ma tsawwalar farashin amfanin yau da kullum da bunkasar miyagun laifuka tun bayan canjin mulkin da aka samu a fadar mulki ta Nairobi misalin shekaru biyun da suka wuce."

A can kasar Ruwanda gwamnati ta haramta ayyukan wasu kungiyoyin da ake zarginsu da yayata akidar kisan kare-dangi a kasar. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Dalilin wannan shawara da gwamnati ta tsayar shi ne sabbin hare-haren da ake kaiwa akan mutanen da suka tsira da ransu daga matakin nan na kisan kare dangi da ‘yan Hutu suka dauka kan ‘yan Tutsi misalin shekaru goma da suka wuce. An fara fuskantar barazanar hare-haren ne tun bayan da gwamnati ta saki dubban masu laifukan kisan daga gidajen kurkuku da kuma damar da wasu dakarun sa kai na Hutu suka samu domin komawa gida. Da yawa daga cikin wadannan masu laifuka suna tsoron shaidar da za a bayar akan laifukansu ne a karkashin kotunan nan na sulhu da aka gabatar a duk fadin kasar Ruwandar. To sai dai kuma kungiyoyi da dama na kasa da kasa, kamar kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Amnesty suna korafi game da wannan mataki na gwamnati a Kigali."

A wannan makon Kungiyar Tarayyar Afurka ta gabatar da taron kolinta a Addis Ababa, inda a cikin jawabin da ya gabatar ga mahalarta taron sakatare-janar na MDD Kofi Annan yayi gargadi a game da mawuyacin halin da ake ciki a kasar Sudan. Jaridar Süddeutsche Zeitung ta gabatar da rahoto tana mai cewar:

"Yakin basasar da ake fama da shi a lardin Darfur na kasar Sudan tun abin da ya kama daga watan fabarairun shekara ta 2003 zai zama babban zakaran gwajin dafi ga Kungiyar Tarayyar Afurka game da tura jami’an sa ido da dakarun kiyaye zaman lafiya zuwa yankin. Domin kuwa a zamanin baya tsofuwar Kungiyar Hadin Kan Afurka OAU ba ta tsoma baki a al’amuran cikin gida na kasashen Afurka sai dai kawai ta zura ido tana kallon ta’asa iri dabam-dabam dake wanzuwa akan talakawan kasashen da lamarin ya shafa."

Kasar Namibiya ta fara yin koyi da makobciyarta Zimbabwe wajen kwace filayen noma na farar fata domin danka su ga hannun bakar fatar kasar, kuma kamar yadda mujallar Der Spiegel ta nunar, tuni wani rukunin farko na Jamusawan Namibiya suka fara yin kaura. Mujallar sai ta kara da cewar:

"Daidai da kasar Zimbabwe, ita ma Namibiya ta tsayar da shawarar kwace gonakin farar fata domin mika su ga tsaffin dakarun neman ‘yancin kasar saboda rawar da suka taka bisa manufa. Wadannan dakarun kuwa kusan dukkansu ‘yan kabilar Ovambo ne. A dai halin da ake ciki yanzu farar fata ‘yan kalilan ne ke da niyyar jan daga domin hana wanzuwar matakin kwace gonakin nasu. A takaice dai kasar Namibiya na fuskantar barazanar baraka tsakanin bakake da farar fatar kasar inda za a shiga wani yanayi irin shigen na kasar Zimbabwe, a maimakon sulhu da cude-ni-in-cude-ka da juna."