1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka a Jaridun Jamus

April 23, 2004

Mawuyacin halin da ake ciki a Darfur ta yammacin Sudan shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan mako

https://p.dw.com/p/Bvq1
'Yan gudun hijirar Sudan dake kwarara zuwa Chadi
'Yan gudun hijirar Sudan dake kwarara zuwa ChadiHoto: AP

A wannan makon mai karewa dai babbar matsalar da ta fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus akan al’amuran Afurka shi ne halin da ake ciki a kasar Sudan dangane da abin da suka kira wai matakan tsaftace kabila da kuma gudun hijirar dubban daruruwan jama’a daga yankunansu na asali. A lokacin da take gabatar da nata rahoton jaridar Die Zeit cewa tayi:

"Wani abin mamaki shi ne kasancewar daga baya-bayan nan ne duniya gaba dayanta tayi juyayin mutane kimanin dubu dari takwas da ta’asar kisan kare dangi ta rutsa dasu a kasar Ruwanda misalin shekaru goma da suka wuce tare da cin alwashin daukar dukkan matakai na hana sake wanzuwar irin wannan ta’asa, amma sai ga shi an sake yin ko oho da wata sabuwar ta’asar ta kisan kare dangi dake wanzuwa a Darfur ta kasar Sudan. To sai dai kuma duk wanda yayi bitar lamarin da idanun basira ba zai yi mamakin ko in kula da ake yi da wannan mummunan ci gaba ba. Dalili kuwa shi ne kasar Sudan ba ta da wani muhimmanci, walau ta fuskar tsaro ko ta tattalin arziki ga kasashen yammaci, ballantana maganar rikicin ta shiga kanun rahotannin kafofin yada labaran kasashen."

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung ta gabatar da sharhi akan kashe-kashen gilla da ta’asa iri dabam-dabam dake wakana a yammacin kasar Sudan, inda ta kara da cewar:

"Wasu rahotanni daga majiyoyi amintattu dake da nasaba da hukumar MDD akan hakkin dan-Adam sun nuna cewar a yankin yammacin Sudan ana fama da ta’asa da keta haddin dan-Adam mafi muni a wannan zamanin da muke ciki yanzun. Ta’addanci da kisan kare dangi tuni suka zama ruwan dare a wannan yanki kuma mahukunta a fadar mulki ta Khartoum sun ki ba wa wakilan MDD wata dama ta kai ziyara lardin Darfur domin gane wa idanuwansu irin halin da ake ciki."

A makon jiya ne aka gudanar da zabe karo na uku a demokradiyyance a kasar Afurka ta Kudu. Mujallar Focus tayi amfani da wannan dama domin bitar halin da ake ciki a kasar ta fuskar siyasa da tattalin arziki. Mujallar sai ta ci gaba da cewar:

"Kasar Afurka ta Kudu ta shiga wani kyakkyawan yanayi na zaman cude-ni-in-cude-ka tsakanin dukkan jinsuna da kabilun kasar. Tsarinta na mulkin demokradiyya na tafiya salin-alin ba tare da tangarda ba, inda kowane jinsi ko kabila ke da wakilansa a majalisar dokoki. Ita kuma gwamnati tana bakin kokarinta wajen kayyade yawan bashin da ta saba karba domin cike gibin kasafin kudinta fiye ma da yadda lamarin yake dangane da kasashen Turai. Wannan manufa ta taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Afurka ta Kudu da sassauta faduwar darajar takardun kudinta. A baya ga dubban daruruwan ‘yan yawon bude ido dake kwarara zuwa kasar, su kuma manyan kamfanoni kamarsu DaimlerChrysler ba sa sako-sako wajen zuba dubban muliyoyi na kudaden jari a wannan kasa, wacce ta dawo daga rakiyar manufofin wariyar jinsi da banbancin launin fata misalin shekaru goma da suka wuce."

To sai dai kuma duk da wannan kyakkyawan ci gaba kasar na fuskantar barazana game da makomarta dangane da yadda cutar nan ta Aids mai karya garkuwar jikin dan-Adam ke dada yaduwa tsakanin al’umarta, lamarin dake addabar kamfanoni da dama dake gudanar da ayyukansu a kasar a cewar jaridar Der Tagesspiegel, wacce ta kara da cewar:

"A hakika ba kasar Afurka ta Kudu ce kadai ke fama da matsalar yaduwar cutar Aids ba, amma ita ce daya kwal da wannan cuta ke barazana ga makomar ayyukan masana’antunta. Kimanin mutane miliyan biyar da dubu dari uku ne ke dauke da kwayar cutar a Afurka ta Kudun, kuma sai da aka yi shekaru da dama kafin gwamnati ta canza manufofinta domin agaza wa kamfanonin, inda ta fara raba magunguna kyauta da kuma bude cibiyoyi domin jiyyar masu cutar, wacce take cinye kimanin kashi 0,5% na bunkasar da kasar ke samu a shekara."