1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka a Jaridun Jamus

April 2, 2004
https://p.dw.com/p/Bvq4

Daya daga cikin muhimman batutuwan da suka fi
daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a
wannan makon mai karewa dai shi ne halin da ake
ciki a kasar Ruwanda, shekaru goma bayan
ta'asar kisan kiyashin da ta wanzu a wannan
kasa dake can kuryar tsakiyar nahiyar Afurka. A
lokacin da take gabatar da rahotonta game da
haka jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:
"Kasar Ruwanda dake kuryar tsakiyar nahiyar
Afurka tayi koyi da matakin da tsofon shugaban
kasar ATK ma'abuci dattako Nelson Mandela ya
dauka lokacin da ya dare kan karagar mulki a
shekarar 1994, inda bai yi wata-wata ba wajen
neman dinke barakar da mulkin wariya ta haifar
yana mai kirkiro kwamitin nan na tsage gaskiya.
To sai dai kuma ko da yake gwamnatin Ruwanda
tana bakin kokarinta wajen samar da kusantar
juna tsakanin 'yan Hutu masu alhakin ta'asar
kisan kare dangin da kuma 'yan Tutsi, wawadnda
ta'asar ta rutsa da su, amma ana fama da
tafiyar hawaniya, saboda su 'yan Hutun suna
daridari wajen rokon gafara, ballantana su kuma
'yan Tutsin su yafe musu wannan dayyen aikin da
suka aikata."
A sakamakon mutuwar mutane tsakanin 25 zuwa 160
a karkashin wani matakin da aka dauka na
murkushe wata zanga-zangar lumana a birnin
Abidjan a makon da ya gabata, dukkan 'yan
tawaye da masu hamayya da manufofin gwamnati a
kasar Cote d'Ivoire sun yi kiran katsalandan
sojojin ketare a rikicin kasar da ya ki ci ya
ki cinyewa, kamar yadda jaridar Die
Tageszeitung
ta rawaito ta kuma kara da cewar:
"Murna ta koma ciki dangane da taron hadin kan
kasa da gwamnati ta kira a kokarin da ake yi na
dinke barakar da kasar Cote d'Ivoire ke fama da
ita bayan da sojoji masu rufa wa gwamnatin
shugaba Laurent Gbagbo baya suka halaka mutane
kimanin 160 dake zanga-zangar neman zaman
lafiya a birnin Abidjan makon da ya gabata. A
daya bangaren kuma MDD tayi alkawarin fara
tsugunar da sojojinta na kiyaye zaman lafiya su
kimanin dubu shida a kasar ta Cote d'Ivoire tun
daga karshen wannan mako domin aiki kafada da
kafada da sojojin kasar Faransa su dubu biyar
da kuma na kasashen yammacin Afurka dake sa ido
akan aikin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka
cima tsakanin gwamnati da 'yan tawaye da kuma
tabbatar da ganin cewar shugaba Gbagbo ya
aiwatar da canje-canjen da aka cimma daidaituwa
kansu tsakaninsa da 'yan tawayen shekarar da ta
wuce."
Nan da makonni biyu masu zuwa ne za a gudanar
da zaben majalisar dokokin Afurka ta Kudu kuma
jam'iyyar ANC ta shugaba Thabo Mbeki tana
fuskantar barazanar kwasar kashinta a hannu,
kuma a saboda haka ya zama wajibi, shugaban mai
shekaru 61 da haifuwa, ya canza salon kamun
ludayinsa a dangantakarsa da al'umar kasar
bakar fata a cewar jaridar kasuwanci ta
Handelsblatt, wacce ta kara da cewar:
"A maimakon daridari da yake yi da mutane a
zamanin baya, a yanzu shugaba Thabo Mbeki na
ATK ya canza take-takensa, inda ya shiga
musafaha da talakawa da kuma sauraron
kararrakin da dayawa daga bakar fata ke dauke
da shi dangane da matsalar muhallin zama da
kuma hauhawar farashin kaya. Dalilin wannan
canji kuwa shi ne barazanar kaurace wa zaben da
ake haufi ta yadda ANC zata yi asarar kashi
biyu bisa uku na magoya bayanta. Jam'iyyar, ko
da yake tana ikirarin cewar tun abin da ya kama
daga 1995 zuwa yanzu ta samar da guraben aikin
yi ga mutane kimanin miliyan biyu, amma fa har
yau akwai matasa dake fama da rashin aikin yi
bayan an yayesu daga makarantu."
Ita ma mujallar Der Spiegel ta leka ATK domin
tsegunta wa masu karatu yadda Jamusawa ke
kwarara zuwa kasar domin kaka-gida a cikinta.
Mujallar sai ta kara da cewar:
"A halin yanzu haka sama da Jamusawa dubu dari
ke zaune a garin Cape Town, a baya ga wasu dubu
140 dake kwarara zuwa garin domin yawon bude
ido a duk shekara. A wani lokacin ma yawan
Jamusawa da kan kutsa garin Cape Town domin
zama na gajeren lokaci ya fi yawan mazauna
birnin Bonn."