1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka a Jaridun Jamus

January 23, 2004
https://p.dw.com/p/BvqD
A wannan makon dai jaridun na Jamus sun mayar da hankalinsu ne kacokam wajen gabatar da rahotanni da sharhuna akan ziyarar aiki ta farko da shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ke yi ga kasashen Afurka, wacce a yau zata kai shi kasar Ghana, zangonsa na karshe, bayan balaguron da yayi a kasashen Habasha da Kenya da kuma Afurka ta Kudu. A lokacin da take bayyana ra'ayinta a game da wannan ziyara jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:
"Ko da yake ba wani dake da takamaiman maganin da zai taimaka a warkar da tabon da nahiyar Afurka ke fama da shi dangane da matsalolin dake addabar kasashenta, amma shirin da aka tanadar a game da yankunan da shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder zai kai wa ziyara abu ne dake yin nuni ga sauyi mai ma'ana ga manufofin Jamus dangane da nahiyar Afurka, bisa sabanin yadda lamarin ya kasance a zamanin baya. Ainifin dalilin wannan ziyarar dai, kamar yadda aka ji daga bakin shi kansa Schröder shi ne domin tabbatar da tsaro a wannan nahiya dake makobtaka da Turai. Jamus na da kyakkyawar niyya ta taimaka wa Afurka a kokarinta na magance rikice-rikicen dake addabar kasashenta. Kuma kowace daga cikin kasashen Afurka da ta gabatar da nagartattun matakai na canje-canjen manufofinta to kuwa ba shakka zata samu cikakken goyan baya daga kasar ta Jamus."
Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:
"Da farkon fari dai murna ta koma ciki dangane da wadanda suka yi fatan cewar gwamnatin hadin guiwa ta SPD da The Greens zata samar da wani canji na a zo a gani a manufofin Jamus dangane da nahiyar Afurka. Domin kuwa tun bayan da ta kama mulki, gwamnatin Gerhard Schröder tayi watsi ne gaba daya da al'amuran wannan nahiya, inda ta rika kayyade yawan taimakon raya kasa da kasashen Afurka ke samu daga Jamus da kuma rurrufe ofisoshin jakadancinta a wasu kasashe na Afurkan. Ainifin wannan sauyi da aka samu, inda ministan harkokin waje Joschka Fischer ya ziyarci nahiyar har sau uku, a yayinda aka shirya wata ziyarar kuma da shugaban kasa Johannes Rau zai kai a cikin watan maris mai zuwa, a hakika ya zo ne sakamakon fafutukar da ake yi na murkushe ta'addanci tsakanin kasa da kasa. Domin kuwa an lura cewar a duk inda ake zaman dardar 'yan ta'adda kan samu kyakkyawar kafa ta neman mafaka da kuma shirya ayyukansu na ta'addanci. Misali hare-haren ta'addancin da aka kai kasar Kenya, duk an shirya su ne a kasar Somaliya. Sannan bugu da kari kuma rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya da ya ki ci ya ki cinyewa, ya sanya aka fara ba da la'akari da dimbim arzikin man fetur da Allah Ya fuwace wa Afurka.
Ita ma jaridar nan ta kasuwanci da ake kira Handelsblatt ta gabatar da rahoto tana mai cewar:
"Ko da yake shugaban gwamnati Gerhard Schröder yayi kira ga kasashen Afurka da su kawar da shingen ciniki, amma a hakika ba manufofin tattalin arziki ne kadai ke taka rawa ga ziyarar da yake yi ga kasashen Afurka ba. Wannan ziyarar tana mai yin nuni ne da canjin salon tunanin gwamnati a fadar mulki ta Berlin a game da Afurka. Dalilin sauyin alkiblar kuwa shi ne tattaunawa mai zurfi da aka yi tsakanin Jamus da Faransa, inda suka cimma daidaituwa akan karfafa huldodinsu da kasashen Afurka. Domin kuwa muddin aka yi sako-sako da matsalolin nahiyar to kuwa ko ba dade-ko-bajima matsalolin zasu karaso zuwa Turai, inda za a wayi gari kasashen na Turai na fama da dimbim 'yan gudun hijira daga Afurka."
Ita kuwa jaridar Frankfurter Rundschau tana tattare da ra'ayi ne na cewar gwamnati a fadar mulki ta Berlin na fuskantar sabuwar kalubala a manufofinta dangane da nahiyar Afurka. Bisa ga ra'ayin jaridar wajibi ne gwamnati ta canza salon kamun ludayinta ta kuma hakikance da alhakin da ya rataya wuyanta na taimakon raya makomar nahiyar Afurka a maimakon danka al'amuran baki dayansa a hannun Kungiyar Tarayyar Turai.