1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka a Jaridun Jamus

January 16, 2004
https://p.dw.com/p/BvqE
A wannan makon dai muhimmin abin da jaridu da mujallun Jamus suka mayar da hankali kansa shi ne tarihin mulkin mallakar kasar ta Jamus a yankin kudu-maso-yammacin Afurka, wato kasar Namibiya ta yanzu, ta la'akari da samun shekaru ga ta'asar kisan kiyashin da sojojin Jamus suka yi wa 'yan kabilar Herero, wadanda kuma suke neman ganin Jamus ta biya diyyar wannan kisa na kare dangi. A lokacin da take ba da rahoto game da haka mujallar Der Spiegel ta ambaci sarkin gargajiya na kabilar ta Herero Riruako yana mai fadin cewar:

"A yanzun bayan da Jamusawa suka mayar da hankali ga ta'asar kisan kiyashin da suka yi wa Yahudawa da 'yan kabilun Sinti da Roma, tilas ne kuma su sake mayar da hankalinsu ga kisan kare dangin da suka yi wa 'yan kabilar Herero. Sarkin dai na neman ganin an biya 'ya'yan kabilarsa diyyar dalar Amurka miliyan dubu biyu. Kuma tuni ya daukaka kara a gaban wata kotun kasar Amurkan. Jamus dai bata son biyan wannan diyya bisa ikirarin cewar a wancan zamanin matakan da sarkin sarakunan daular Jamus ya dauka ba su saba da tsarin yarjeniyoyi na kasa da kasa ba. Bugu da kari kuma kasar na ba wa Namibiya taimakon raya kasa fiye da sauran kasashe dake samun irin wannan taimako daga Jamus. Amma 'yan kabilar Herero sun dage akan cewar ba su ne ke cin gajiyar wannan taimako ba, sai dai 'yan kabilar Ovambo, wadanda ko da yake ba su yi asarar filaye ko rayuka a hannun Jamusawan ba, amma sune ke da rinjaye a jam'iyyar SWAPO dake mulki."

Daga Namibiya sai mu koma makobciyar kasa ta Zimbabwe, wacce ke fama da matsalar yunwa yanzu haka, amma ake fama da tafiyar hawainiya wajen kai wa al'umar kasar taimakon abinci, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta rawaito ta kuma kara da cewar:

"Kasar Zimbabwe ta sake fadawa cikin matsalar yunwa daidai da yadda lamarin ya taba kasancewa a shekarar da ta wuce. Alkaluma masu nasaba da kungiyoyin taimako sun ce akalla mutane miliyan biyar ne ke bukatar taimakon abinci a yankunan karkara na kasar, a baya ga wasu miliyan daya a manyan garuruwa da biranenta. Akwai mutane da dama dake tattare da imanin cewar bana matsalar zata yi tsamari fiye da ta bara, musamman ta la'akari da tafiyar hawainiyar da ake samu ga matakan taimako na kasa da kasa."

A can kasar Angola, ko da ya ke a misalin shekaru biyun da suka wuce an samu nasarar cimma wata sahihiyar yarjejeniya ta zaman lafiya, amma fa har yau kasar tana fama da tasirin yakin basasarta na tsawon shekaru 30, a cewar jaridar Frankfurter Rundschau a cikin wani dogon rahoton da ta bayar a game da matsalar kasar ta kudancin Afurka. Jaridar sai ta ci gaba da cewar.

"A karo na farko a misalin shekaru biyun da suka wuce al'umar Angola suka fara sanin wani abin da ake kira zaman lafiya. Amma duk wanda ya dubi mawuyacin hali na rayuwa da al'umar kasar ke ciki, zai ga tamkar dai an gudu ne ba a tsira ba, kuma zaman lafiyar na ma'anar dakatar da fada ne kawai amma ba su samu kwanciyar hankali ba. A yayinda akasarin al'umar kasar ke fama da yunwa da kaka-nika-yi, masu fada a ji a al'amuran wannan kasa, kamar yadda wani rahoto mai nasaba da MDD ya nunar, su kan ware abin da ya kai dalar Amurka miliyan dubu daya daga kudaden shiga da kasar ke samu daga cinikin man fetur, domin ajiyarsu a bankunan kasashen ketare."

A wani bangaren kuma jaridar ta Frankfurter Rundschau tayi bitar tasirin kasar Faransa akan kasashen da ta rena a nahiyar Afurka ta amfani da takardun kudin CFA bai daya tsakaninsu. Jaridar sai ta kara da cewar:

"A sakamakon takardun kudi bai daya da kasar Faransa ta gabatar tsakanin kasashen Agfurka da ta rena tun a shekara ta 1948 kasar ke da ikon tasiri a manufofin siyasa da tattalin arziki da kuma na soja a wadannan kasashe, duk kuwa da cewar sun samu 'yancin kansu daga Faransar tun sama da shekaru arba'in da suka wuce. Kasar ta Faransa ce ke tsayawa takardun kudin na CFA domin musayarsu a ketare, kuma a madadin haka wadannan kasashe suka amince da zuba kashi 65 na kudadensu na musaya a ma'aikatar kudi ta Faransar."