1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

Ahmed Tijani LawalJanuary 9, 2009

Sharhunan Jaridu n Jamus akan Afrika

https://p.dw.com/p/GV9Q
LagosHoto: AP

Nigeria/Ghana/Congo


Nigeria

Da farko zamu fara ya da zango ne a Lagos cibiyar kasuwancin Nijeriya, inda aka fara samun canjin al'amuran sufuri a yanzu haka, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta nunar. Jaridar ta ce:

"A yanzu mazauna birnin Lagos, daya daga cikin birane da suka fi girma da cunkoson jama'a a nahiyar Afurka, suna iya yin Hamdala, saboda akwai sabbin motocin safa, wadanda za su iya kai mutum har wurin da zai sauka ba tare da an tsangwame shi ko an yi masa sata ba. Wannan sabuwar dabara da gwamnatin jihar Lagosd ta kirkiro ka iya zama abin koyi ga sauran manyan biranen Afurka masu fama da cunkoson jama'a da tabarbarewar al'amuran sufuri, inda aka samar da sabbin motoci na bus, wadanda aka kebe musu hanyoyin zirga-zirga na musamman domin damar kai da komo ba tare da wahala ba. Sai dai kuma sauran kamfanonin sufuri masu zaman kansu sun fara gunaguni saboda sabbin motocin na gwamnati zasu kashe musu kasuwa."

Ghana

A kasar Ghana dai an samu canjin gwamnati a cikin ruwan sanyi, inda aka nada sabon shugaba farfesa Atta Mills dan jam'iyyar hamayya ta NDC sakamakon nasarar da ya samu kan abokin takararsa Nana Akufo-Addo dan jam'iyyar NPP da tayi mulki a zaben fid da gwanin da aka gudanar makon jiya. A lokacin da take sharhi akan haka jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

John Atta Mills - Wahlen in Ghana
John Atta MillsHoto: AP

"Kasar Ghana dake yammacin Afurka kasa ce da aka santa da zaman lafiya tun shekaru aru-aru da suka wuce, ko da yake an shiga wani hali na dardar sakamakon kunnen dokin da aka yi tsakanin manyan 'yan takarar da suka tsaya zaben neman zama shugaban kasa a zagayen farko ranar bakwai ga disemba da kuma zagaye na biyu a ranar 28 ga wannan wata. Ita jam'iyyar NPP ba ma kawai asarar zaben shugaban kasa tayi ba, kazalika tayi asarar rinjayen da take da shi a majalisar dokoki. Al'amura dai sun tafi salin-alin, inda a bayan rikice-rikicen da aka fuskanta a kasashen Kenya da Zimbabwe, zaben Ghana ya zama wani zakaran gwajin dafi ga makomar demokradiyya a Afurka."

Congo

Har yau ana ci gaba da farautar 'yan tawayen Uganda dake shirya hare-harensu daga harabar kasar Kongo. To sai dai kuma a sakamakon rashin nasarar bin diddiginsu da ake yi mutane suka fara korafi a game da wannan mataki na sojan Uganda a kasar Kongo. Jaridar Die Tageszeitung tayi sharhi tana mai cewar:

Zusätzliche Kongo Truppen möglich
Janhuriyar Demokraɗiyyar KongoHoto: picture-alliance/ dpa

"Har yau 'yan tawayen Uganda na kungiyar LRA na ci gaba da aikata mummunar ta'asarsu ta kashe-kashen kiyashi, a yayinda dubban sojojin da Uganda ta tura domin farauta da karya alkadarinsu ba su cimma nasara ba. Kawo yanzun ba wanda ya san mafakar Kony madugun 'yan tawayen tun bayan da aka ragargaza shelkwatarsa dake kasar Kongo. Rahotannin dake cewar wai ya tsere zuwa janhriyar Afurka ta Tsakiya tana iya yiwuwa ba kome ba ne illa wata dabara ta kawar da hankali, saboda a yanzu kuma akwai wasu rahotannin dake cewar wai yana can kusa da iyakar Kongon da Sudan. Ana dai korafi game da cewar dalilin rashin nasarar matakin shi ne kasancewar shugaba Museveni ta wayar tarfo ne yake ba da oda."