1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

Mohammad AwalFebruary 9, 2009

Sharhunan Jaridun Jamus game da nahiyar Afurka

https://p.dw.com/p/GpoU
Shugaba Ghaddafi a taron ƙolin AUHoto: AP

Daga cikin batutuwan da suka ɗauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon har da halin da ake ciki a Zimbabwe inda gwamnatin ta yaba wa dan hamayya Morgan Tsvangirai a game da shawarar da ya tsayar na shiga a dama da shi a al'amuran mulki. To sai dai kuma duk da haka ƙungiyar tarayyar Turai ta ce bata da niyyar taimakawa da kuɗi, a yayin da ba a tantance yadda za a raba madafun iko a ƙasar ba. A lokacin da take sharhi game da haka jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

Zimbabwe

Zimbabwe Morgan Tsvangirai Pressekonferenz
Morgan Tsvangirai jagoran ´yan adawa a ZimbabweHoto: AP

"A sakamakon salon kamun ludayin shugaba Mugabe a halin yanzu haka Zimbabwe na fama da fatara. Darajar takardun kuɗin ƙasar ta faɗi warwas, a yayinda kimanin kashi 94 cikin 100 na al'umarta ke zama hannu-baka-hannu-ƙwarya. Kuma ko da yake gwamnati na fatan samun taimako daga Ƙungiyar Tarayyar Turai sakamakon daidaituwar da aka cimma na raba madafun iko, amma fa ƙungiyar a nata ɓangaren tana kan bakanta na ƙin ba da taimako ko anini matsawar da shugaban babban bankin kasar ta Zimbabwe Gideon Gono ya ci gaba akan muƙaminsa."

AU/Addis Ababa

BdT Libyen Muammar Gaddhafi mit Afrika Hemd
Muammar Gaddhafi shugaban AU a yanzuHoto: AP

A taron ƙolinsu na Addis Ababa a wannan makon shuagabannin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Afurka AU sun naɗa shugaban Libiya Muammar Gaddafi sabon shugaban ƙungiyar. Jaridar Berliner Zeitung tayi sharhi tana mai cewar:


"Wani abin lura game da taron ƙolin shi ne kasancewar an fi mayar da hankali ne wajen tattauna shawarar da Gaddafi ya mayar game da kafa wata haɗaɗɗiyar daula ta Afurka, a maimakon ainihin alƙiblar taron wadda ta shafi zuba jari domin kyautata al'amuran sadarwa a nahiyar Afurka. Sakamakon taron dai bai taka kara ya karya ba, inda aka cimma daidaituwa akan canza wa kwamitin zartaswa ta ƙungiyar AU suna zuwa hukumar ƙasashen Afurka mai ƙunshe da sakatarori a maimakon kwamishinoni. Sai dai kuma an kammala taron ba tare da an fayyce matakan da za a ɗauka don cimma burin da aka sa gaba na kafa haɗaɗɗiyar daular Afurka ba."

Sudan

Sudan Präsident und Internatinaler Strafgerichtshof Montage
Shugaban Sudan Omar al-BashirHoto: AP / dpa / DW

Ko da yake ƙasar Sudan, ƙasa ce dake fama da rikici iri daban-daban, amma kuma a ɗaya hannun tana samun bunƙasa matuƙa ainun, kamar yadda jaridar Süddeutsche Zeitung ta nunar ta kuma ƙara da cewar:

"Akasarin masu zuba jari a ƙasar Sudan 'yan kasuwa ne daga ƙasashen gabas mai nisa, musamman ma daga ƙasar China da kuma ƙasashen Larabawa. Hatta takunkumin karya tattalin arzikin ƙasa da Amurka ta ƙaƙaba wa Sudan tun tsawon shekaru da dama da suka wuce bisa tuhumarta da mara wa 'yan ta'adda baya, ba ja birki ga bunƙasar da Sudan take samu ga tattalin arzikinta ba. Bayan da kamfanonin ƙasashen Turai suka janye, sai na wasu ƙasashen suka maye gurbinsu. 'Yan kasuwar Sudan sai kaɗa kai suke suna mamaki a duk lokacin da aka yi batu game da takunkumin na Amurka, wanda a halin da ake ciki yanzu haka ba shi da wani tasiri na a zo a gani a kasar."