1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka ta Kudu ta samu kyakkyawan ci gaba a cikin shekaru goma da suka wuce

April 16, 2004

Halin da ake ciki a Afurka ta Kudu, shekaru goma bayan kifar da mulkin wariya da kuma zaben demokradiyya da aka gudanar karo na uku a kasar, shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan mako

https://p.dw.com/p/Bvq2
Miliyoyin mutane suka yi cincirindo domin kada kuri'a a zaben kasar Afurka ta Kudu a wannan mako
Miliyoyin mutane suka yi cincirindo domin kada kuri'a a zaben kasar Afurka ta Kudu a wannan makoHoto: AP

A yayinda a makon da ya gabata jaridu da mujallun Jamus suka mayar da hankalinsu kacokam akan zaman juyayin da aka yi domin tunawa da ta’asar kisan kiyashin da aka fuskanta a kasar Ruwanda shekaru goma da suka wuce, a wannan makon jaridu da mujallun sun ba da la’akari ne da halin da ake ciki a kasar Afurka ta Kudu (ATK), shekaru goma bayan gusar da mulkin wariyar jinsi a wannan kasa da kuma dorata da aka yi akan sahihin tsari na demokradiyya, inda a wannan makon aka gudanar da zabe karo na uku a kasar. A lokacin da take ba da nata rahoton jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

"Kasar Afurka ta kudu ta samu kyakkyawan ci gaba a cikin shekaru goman da suka biyo bayan mulkin wariyar jinsi ta tsiraru farar fata. Kasar ta fuskanci juyin juya hali har sau uku a tsakanin wadannan shekaru goma. Da farko, a cikin lumana da kwanciyar hankali, ta samu canjin manufofinta daga kama karya ta farar fata masu wariyar jinsi zuwa tsarin mulki na demokradiyya dake kamanta adalci tsakanin kowa-da-kowa. Na biyu kasar ta kawar da shingen ciniki tana mai kakkabe hannuwanta daga matakan karya farashin kaya dake mummunar illa ga tattalin arzikinta. Sannan na uku kasar ATK ta sabunta tsarin kasuwarta ta kodago, wacce a da ta dogara kacokam akan ayyukan noma da albarkatun kasa. Wannan a hakika abu ne da ya cancanci yabo."

Ita kuwa jaridar Frankfurter Rundschau tayi bitar nasarorin da ATKn ta cimmusu ne a manufofinta na ketare a cikin shekaru goman da suka wuce. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Tuni dai ATK ta karfafa matsayinta na kasancewa babbar daula a nahiyar Afurka. Wannan nasarar abu ne da ya cancanci yabo ta la’akari da shekaru masu yawa da tayi tana mai bin manufofi na tayar da zaune tsaye a kasashen dake makobtaka da ita a karkashin mulkinta na wariyar jinsi. A cikin shekaru goma kacal kasar ta warkar da kanta daga wannan tabo tana mai karfafa huldodin tattalin arzikinta da kasashen Turai da Amurka. A baya ga haka kasar ta kara fadada alakarta da kawayenta na gamayyar tattalin arzikin kudancin Afurka SADC. A nan ba za a manta da rawar da take takawa wajen sasanta rikice-rikicen da suka zama ruwan dare a sassa dabam-dabam na Afurka ba da kuma yadda ta zama ja-gaba wajen yayata manufar sake farfado da al’amuran Afurka da ta da komadar tattalin arzikinta a karkashin abin da aka kira Sabon Kawancen Raya Nahiyar Afurka (NEPAD) a takaice."

‘Yan tawayen Hutu sun sake wani sabon yunkuri na neman tayar da zaune tsaye a gabacin kasar Kongo, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta nunar, ta kuma kara da cewar:

"Ko da yake kusan kashi 50% na dakarun tawayen Hutu suka amince da tayin ajiye makamai, amma har yau akwai wasu ‘yan tsagera masu taurin kai da suka lashi takobin ci gaba da fafatawa har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi. Wannan sabon hali mawuyaci da aka shiga yayi kicibis da manufar kara yawan sojan kiyaye zaman lafiya na MDD a gabacin Kongo. Mazauna yankin sun saka dogon buri akan sojojin na MDD su 3 700 a game da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kimanin mutane miliyan daya da dubu 400 aka fatattakesu daga gidajensu a larduna uku na gabacin Kongo. Kuma a sakamakon matakai na ta’addancin da ‘yan sare ka noken ke dauka babu wata kafa ta kai musu kayan taimako."

Bisa ga ra’ayin shugaban kwamitin nazarin matakan soja na kungiyar tarayyar Turai mai yiwuwa kungiyar ta tura sojojinta na kiyaye zaman lafiya zuwa yammacin Sudan idan har zarafi ya kama. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar Der Tagesspiegel cewa tayi:

"Sama da mutane dubu 10 suka rasa rayukansu sakamakon fadan da ya ki ci ya ki cinyewa a lardin Dafur dake yammacin kasar Sudan. An fatattaki mutane dubu 670 daga gidajensu sannan wasu sama da dubu dari suka nemi mafaka a makobciyar kasa ta Chadi. Tuni MDD take batu a game da wani mataki na tsabtace kabila tana mai dora alhakin lamarin akan mayaka na Larabawa dake samun goyan baya daga fadar mulki ta Khartoum."