Ahmadinejad yace matsin lamban ƙasashen Duniya na karfafa musu gwiwa
April 3, 2010Talla
Shugaba Mahmoud Ahamedinejad ya bayyana cewar, cigaban matsin lamban da Duniya take wa Iran, da suka haɗa da yiwuwar kakabawa mata sabbin takunkumi, su ne ke daɗa karfafa mata kwarin gwiwa wajen cigaba da shirin inganta makamashinta na nukiliya. Waɗannan kalamai nasa dai sun zo ne, bayan da shugaba Barack Obama ya lashi takobin tabbatar da matsin lamban manyan ƙasashen Duniya akan Tehran, domin ganin cewar tayi watsi da shirinta na bunkasa sinadran Atom, wanda a cewarsa keda nufin kera makaman Nukiliya. A halin da ake ciki yanzu haka dai, babban jami'in kula da harkokin bunkasa Atom a Iran Ali Akbar Saleh, yace an mikawa shugaba Ahmedinejad bukatun gina sabbin cibiyoyi bunkasa Uranium guda biyu a ƙasar.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Yahouza Sadissou