1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ahmedinejad ya isa Nicaragua

January 14, 2007
https://p.dw.com/p/BuUW

A rangadin aikin daya fara na neman goyon bayan kasashen yankin latin Amurka,shugaba Mahmoud Ahmadinejad na kasar Iran ya kasa kasar Nicaragua,Kasar da shugaba Daniel Ortega,wanda ke sukan lamirin Amurka ya sake komowa madafan iko.A ranar larabar data gabata nedai aka rantsar da Ortega a matsayin shugaban kasa a Nicaragua,inda yayiwa alummomin kasar alkawuran aiwatar da shiye shiryen yaki da talauci.Manazarat dai na ganin cewa,Iran dake da dumbin arzkin man petur zata iya taimakaw Mr Ortega adangane da waddana manufofi nasa.Duk dacewa shugaba Amhamedi nejad ya isa birnin Managua cikin dare ne,shugaba Ortega dashi da manyan jamian gwamnatin kasar suka karbr shi a filin saukan jiragen sama.A jiyan nedai shugaban na Iran ya fara wannan rangadin aikin nasa na kasashen Latin Amuj´rka da birnin Carakas,inda ya gana da shugaba Hugo Charvez.Shugabbanin biyu dai sun hakikance cewa ,Iran tana da hakkin inganta juyin juya hali na duniya baki daya.Ziyarar tasa dai zata kaishi zuwa kasashen Ecuador da kuma Bolivia.