1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin Bauta wa Ƙasa na Farar Hula

November 18, 2009

Gwamnati na shawarar ƙayyade lokacin aikin sojan bauta wa ƙasa, lamarin da zai yi tasiri akan aikin bauta wa ƙasa na farar hula a Jamus.

https://p.dw.com/p/KaCD
Aikin farar hula na bauta wa ƙasa a JamusHoto: DW / Julia Carneiro

Doka a nan Jamus ta tanadi aikin sa kai na farar hula ga duk wanda yaƙi shiga aikin soja na bauta wa ƙasa. A halin da muke ciki yanzu haka matasa maza kimanin dubu 70 ne ke gudanar da wannan aiki, inda suke kula da marasa lafiya da naƙasassu da kuma tsofaffi. Amma sabuwar gwamnati a fadar mulki ta Berlin ta tsayar da shawarar ƙayyade tsawon lokacin aikin sojan bauta wa ƙasa zuwa watanni shida, a maimakon watanni tara, lamarin dake ma'anar ƙayyade lokacin aikin sa kai na farar hula kai tsaye. A sakamakon haka ƙungiyoyin taimako da lamarin ya shafa suka fara kokawa da lamarin.


A cikin wani bayani da tayi, Gabriele Thivissen, mai kula da matasa dake aikin bauta wa ƙasa na farar fula a ƙungiyar taimako ta red cross a jihar Northrhjine-Westfaliya, a game da ire-iren matsalolin da wannan matakin zai haifar, nuni tayi da cewar:


"Ba shakka zamu sha fama da raɗaɗin tasirin wannan ci gaba, idan har gwamnati ta dage akan mayar da matakin nata doka".

Symbolbild Zivildienst - Hilfskraft beim Arbeiter- Samariter-Bund
Kimanin matasa 850 ke aikin bauta wa ƙasa ƙarkashin tutar red cross a jihar Northrhine-WestfaliyaHoto: dpa


A dai halin da muke ciki yanzu haka kimanin matasa 850 ke gudanar da ayyukansu ƙarƙashin tutar reshen ƙungiyar tata a jihar Northrhine-Westfaliya. Amma idan har an ƙayyade tsawon lokacin aikin zuwa watanni shida, za a wayi gari aikin gaba ɗaya ba shi da alfanu, in ji Gabriele Thivissen, a hirar da ta gudanar da tashe Deutsche Welle:


"A kai yi watanni uku ana ba su horo a ɓangaren da zasu gudanar da ayyukansu kafin a rarraba su zuwa yankunan da zasu gudanar da ayyukan nasu. Amma a ƙarƙashin wannan sabon mataki ba zasu samu wata kafa ta gudanar da aikinsu ba ke nan".


Ayar tambaya a nan ita ce ta yaya za a cike wannan giɓi? Ulrike Mascher, shugabar gamayyar ƙungiyoyin taimako na farar hula a Jamus, ta bayyana fargabar cewar ƙayyade tsawon lokacin aikin zai fi shafar majiyyata da naƙasassu.


"Galibi ɗalibai dake fama da naƙasa ba sa iya zuwa aji sai tare da rakiyar masu aikin farar hula na bauta wa ƙasa. Amma idan ya zama ana samun canji a bayan ko waɗanne watanni shida zai zama matsala gare su saboda neman sabo".


Wajibi ne dai a fahimta cewar kawo irin wannan canji zai haifar da matsaloli, musamman na kuɗi ta yadda zai zama tilas daga ɓangaren masu ɗaukar nauyin taimakon da kuma gwamnati su ɗauki matakai na tsumulmular kuɗi. Tuni ma dai wasu kafofin suka fara bayyana shirinsu na dakatar da wasu ayyukan ko kuma a riƙa ba wa masu aikin bauta wa ƙasar wasu ayyukan irin na lebura ta yadda nan gaba za a wayi gari ba wani mai sha'awar kama irin wannan aiki na bauta wa ƙasa. Tun dai abin da ya kama daga shekara ta 1955 ya zama wajibi akan 'ya'ya maza da suka cika shekaru 18 na haifuwa a nan Jamus su kama aikin soja na bauta wa ƙasa. Duk kuma wanda ke ƙayamar aikin soja saboda wasu dalilai da yake ganin hakan bai dace ba, yana da ikon kama aikin bauta wa ƙasa na farar hula. A zamanin baya aikin na soja na ɗauki tsawon watanni 18 a yayinda na farar hula kuma ke ɗaukar watanni 20. Amma ganin yadda ake samun ƙaruwar yawan matasa dake ƙayamr aikin sojan sai aka ƙayyade dukkan ayyukan guda biyu zuwa watanni tara. Amma shawarar gwamnati game da ƙayyade aikin sojan bauta wa ƙasa zuwa watanni shida shi ne domin shawo kan matasa suke karkata zuwa ga wannan manufa.