1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin ceto naci gaba da gudana a Bad Reichenhall dake nan Jamus

January 3, 2006
https://p.dw.com/p/BvDx

Yawan mutanen da suka rasa ransu a garin Bad Reichenhall dake jihar Beberiya a nan Jamus sakamakon fadowar rufin zauren wasanni kann kankara, a yanzu haka sun kai mutane 11.

Rufin wanda ya fado a sakamakon yawan kankara, ya zuwa yanzu, Jami´an bayar da agajin gaggawa sun shaidar da cewa sun samu galabar ceto mutane 35, amma wasu daga cikin su sun jikkata kwarai da aniya.

Wannan hatsari ya auku ne a dai dai lokacin da ake tsammanin mutane kusan hamsin na cikin zauren wasannin.

Ana dai kyautata zaton cewa nan gaba kadan yawan mutanen da suka rasa rayukan nasu ko kuma suka jikkata ka iya karuwa.

A waje daya kuma, rahotanni sun nunar da cewa masu gabatar da kara na jihar ta Beberiya na tunanin gabatar da kara a gaban kuliya akan laifi na sakaci, bisa tunanin cewa hakan nada nasaba da faruwar wannan hatsari.