1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin ceto ya kankama a Bangladesh

November 17, 2007
https://p.dw.com/p/CIRy
An ƙaddamar da wani gagarumin aikin agaji sakamakon guguwar nan mai ƙarfi haɗe da ruwan sama da ta yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane dubu ɗaya da 600 sannan ta jikata dubu 15 a kasar Bangladesh. Datti da ambaliyar ruwa na kawo cikas ga aikin ceto musamman a yankunan karkara na ƙasar. Jiragen ruwan soji da jiragen sama masu saukar ungulu na ƙokarin kaiwa ga dubu dubatan mutane da suka tsira don kai musu abinci da magunguna da suke bukata ruwa a jallo. A ranar alhamis da daddare guguwar da ake yiwa laƙabi da Sidr ta ratsa Bangladesh tana gudun kilomita 250 cikin awa daya. Ta lalata gidaje masuy awan gaske sannan ta ajnyo katsewar wutar lantarki tare da yin awon gaba da shuke shuke yanzu da ake dab da shiga kaka a wannan ƙasa dake kudancin nahiyar Asiya. Kungiyar tarayyar Turai ta bawa kasar taimakon gaggawa na euro miliyan daya da rabi sannan Jamus ta yi alkawarin ba ta euro dubu 500.