1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin haƙar gas na haɗin gwiwa tsakanin Jamus da Rasha

December 18, 2007
https://p.dw.com/p/CdHB

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier tare da mataimakin firaministan Rasha Dmitry Medvedev sun ƙaddamar da wani sabon shirin haɗin gwiwa na haƙar ma’adinan iskar gas a k Rasha.Minista Steinmeier yace Jamus ta gamsu da wannan shiri na tsakanin kanfanin Rasha da kuma BASF na Jamus.Medvedev wanda ake ganin shi zai gaji Vladmir Putin yace wannan shirin wani misali ne na cewa Rasha a shirye ta ke ta haɗa hannun jari da ƙasashen ƙetare haka kuma zata iya bada gudumowa mai muhimmanci a fannin makamashi a turai. Ana sa ran a lokacin ziyarar tasa Steinmeier zai tattauna tare da Medvedev a game da batun take hakkin bil adama a Rasha.