1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin hajj a Saudia naci gaba da gudana lafiya

January 10, 2006
https://p.dw.com/p/BvCz
Yan mata a Sudan - karkashin al'adar shayi
Yan mata a Sudan - karkashin al'adar shayiHoto: dpa

Mahajjata a kasa mai tsarki naci gaba da gudanar da aiyukan hajjin su, bayan da a yammacin jiya suka kammala daya daga cikin jigogin aikin hajji, wato hawan arfa.

Bayanai dai sun nunar da cewa mahajjatan na ci gaba da gudanar da aiyukan nasu ne bisa tsauraran matakan tsaro da mahukuntan kasar suka dauka.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa kusan jami´an tsaro da ma´aikatan lafiya dubu sittin ne aka baza a cikin kasar, a matsayin shirin kota kwana na dakile duk wata matsala ko fitina da ka iya tasowa.

An dai kiyasta cewa mutane sama da miliyan biyu ne ke gudanar da aikin hajjin na bana a kasar ta Saudi Arabia.