1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin jarida cikin halin tasku a Najeriya

Uwais Abubakar Idris
May 3, 2017

Yayin da ake bikin ranar ‘yancin ‘yan jaridu ta duniya, a Najeriya ‘yan jaridu da aikin jaridar kansa na fuskantar kalubale mai yawa kama daga na kashe ‘yan jaridun da takura musu da ma rashin albashi.

https://p.dw.com/p/2cHhG
Nigeria Abuja Mohammadu Buhari Presse
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Curtis

Aikin jarida na daya daga cikin sana'oi masu muhimmanci a duniya abin da ya sanya ake neman kwarewa ta musamman domin gudanar da shi musamman a kasashe irin na Najeriya tare ma da samar da dokoki don kare ‘yan jaridu daga fuskantar cin zarafinsu. To sai dai akwai dimbin matsaloli da ke kawo cikas da gudanar da aikin, wadanda ke kara barazana ga wannan sana'a mai muhimancin gaske, kamar yadda Malam Shuaibu Leman sakataren kungiyar ‘yan jaridun Najeriya ke gani.

Ma'aikatan radiyo na bayar da gagarumar gudunmawa
Ma'aikatan radiyo na bayar da gagarumar gudunmawaHoto: Agnes Leder

Taken bikin na wannan shekara dai shi ne: Rawar da kafofin yada labarai ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya. To sai dai kama daga cin zarafi zuwa ga bi har gida a kashe, na zaman matsaloli da ke fuskantar aikin. Su kansu mata ‘yan jarida na da nasu kalubale da matsaloli na daban da ke kawo masu cikas kamar yadda Malama Aisha Mu'azu ta ce, kasancewa mace ‘yar jarida kan fiskanci cikas a ayyuka a Najeriyar. A hannu guda kuma kara bunkasar shafukan sada zumunta na zamani, na zama sabon kalubale da ke fuskantar aikin jaridar a Najeriyar, musamman yadda wasu ke kallon su a matsayin masu yada labarai na bogi. A yayin da ‘yan jaridun Najeriyar ke bikin ranar ‘yancinsu, suna kuma cike da fatan samun sauyi daga yanayi da suke aiki a yanzu, kasancewar su na da kololuwar muhimmanci bisa ga rawar da suke takawa ga wanzuwar tsarin kasa irin ta Najeriya.