1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AINIHIN ASALIN ANIYAR KASAR LIBYA TA MAKAMIN NUKILIYA

December 24, 2003
https://p.dw.com/p/Bvmx
Kwamitin sulhu na MDD yayi maraba da aniyar kasar Libya na watsi da matakin data dauka na kera makamin nukiliya,tare da cewa wannan mataki ka iya zama wani abin koyi ga sauran kasashen duniya da ake takaddama dasu kann wannan mataki na kera makaman na nukiliya. A cikin wata sanarwa da kwamitin sulhun ya bayar a ranar talatar data gabata ya bukaci,da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya,wato AIEA a takaice datayi gaggawar binciken tabbatar da wannan aniya ta kasar ta Libya,don duba yiwuwar kawo karshen saniyar waren da aka mayar da kasar ta Libya a fagen siyasar duniya,sakamakon takunkumin da aka lakaba mata. A yanzu haka dai tuni wakilan kasar ta Libya suka gudanar da taron koli da jamian hukumar ta makamashin nukiliyar don cimma yarjejeniya game da wannan mataki ta hanyar kyale jamian hukumar ta IAEA gudanar da bincike kann makaman na nukiliyar kasar ta Libya.
A don haka a yanzu haka kwamitin sulhun na mdd yace zai sa ido yaga yadda za,a aiwatar da wannan yarjejeniya da aka kulla a tsakanin mahukuntan kasar ta Libya da kuma jamian hukumar ta IAEA.
Kafin dai kasar ta Libya ta dauki wannan mataki a baya ta shigo da wasu masanane daga kasashen yamma cikin kasar tare da kayan aiki,a aniyar tata ta kera wadan nan makamai na nikiliya,tun da hakikanin gaskiya kasar bata da mutanen da suke da wannan ilimi na kera makaman na nukiliya. A kuwa ta bakin wani jamiin diplomasiyya,kasar ta Libya a tun wancan lokaci,ta shigar da mutanen ta ne izuwa kasar Amurka da kuma wasu kasashe na nahiyar turai don nakaltar yadda ake kera makamin na nukiliya,wanda a shekara ta 1976 kasar faransa ta yarda ta kerawa kasar tashar nukiliya amma mai samar da wutar lantarki a cikin fadin kasar ta Libya baki daya.
A cikin wani rahoto da hukumar leken asirin kasar Amurka ta fitar a watan nuwanba na bara ya nunar da cewa,kasar ta Libya a wancan lokaci tayi amfani da nasaba da take dashi a kasashen waje wajen sayo fusahar kara makamin na nukiliya.
Haka kuma hukumar tace a wata ziyarar ba zata data kai izuwa kasar ya tabbatar mata da cewa kasar nada sanadarin uranium da akeyin nukiliyar dashi. Bugu da kari hukumar ta kuma shaidar da cewa,a baya kasar ta Libya taso tayi amfani da wannan damar wajen hada hodar ibilis mai guba,a shekara ta 1980 a wata masana,anta mai nisan kilomita 40 daga kudu maso yammacin birnin Tripoli.
Wannan dai masana,anta ta Pharma,a cewar rahoton wata cibiya ta bincike a Amurka,an samu damar gano tane a shekarar 1988,kuma an tabbatar da cewa kasar Jamus ce ta kafa ta,tare da samar da kayayyakin cikinta tare da taimakon kasashe irin su Faransa da switzerland da kuma Austria,da sunan za,a bude masana,antar ne a kasar Hong Kong.
A kuwa daya barin a cewar wasu jamian dplomasiyya na kasashen yamma,kasar Pakistan dake da wannan makami na nukiliya taki tace komai dangane da wannan mataki na kasar ta Libya,musanmamma bisa laakari da cewa akwai bayan boye dake nuni da cewa wasu masani ilimin kimiyyar sanin makamar kera nukiliyar kasar ta Pakistan sunyi musayar raayoyi na ilimin da masana ilimin kimiyyar kasar iran,wacce a yanzu haka kasar Amurka ke zargin nada wadan nan makamai na nukiliyar.