1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Airbus ta samu kwangila mafi tsoka

Usman ShehuJune 9, 2010

A wani abinda ke nuna irin yadda harkar jiragen sama ke ƙara bunƙasa , kamfanin jirage na Emirate zai sayi sabbin jirage 32.

https://p.dw.com/p/Nln4
Maƙerar jirage ta AirbusHoto: AP

Kamfanin ƙera jiragen sama na Turai wato Airbus ya samu ƙwangila mafi tsoka a tarihinsa, inda yanzu kamfanin jiragen sama na Emirate mallakar haɗaɗɗiyar daular larabawa, yake son sayan jirage 32, wanda kuɗinsu ya haura dala miliyan dubu goma sha ɗaya. An samu cimma wannan ne a bikin nunin jiragen sama da aka yi a Berlin. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wanda ta buɗe bikin nuni na jiragen saman, ta kwatanta wannan kwangilar a matsayin wata babbar nasa ga kamfanin ƙera jiragen na Airbus. Shugaban kamfanin jiragen sama na Emirate Sheikh Ahmed Bin Sa'id yace yana da imanin cewa kamfaninsa zai  samu bunƙasa, duk da irin tangal tangal na tattalin arzikin duniya, dama batun cikas ɗin da dutse mai aman wuta daga ƙasar Iceland ya haddasa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita. Umaru Aliyu