1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ajendar ziyara Olesegun Obasanjo a kasar Kote Divoire

November 3, 2005
https://p.dw.com/p/BvMg

Gobe ne idan Allah ya kai mu, shugaban Tarayya Afrika Olesegun Obasanjo, zai kai ziyara aiki a kasar Kote Divoire, inda zai gana da wakillai daban daban na bangarori masu gaba da juna a kasar.

Obasanjo, zai tantana tare da su, a kan batun hukunci da Majalisar Dinkin Dunia ta yanke a game da rikicin siyasa, da ke gudana a kasar, a sakamakon kasa cimma daidaiton shirya zaben shugaban kasa ranar 30 ga watan da ya wuce.

Hukunci na Majalisar Dinkin Dunia, ya ba shugaba Lauran Bagbo damar zama bisa kujera mulki, har tsawan watani 12, kamin a yi saban zabe bisa sa idon kungiyar Taraya Afrika da Majalisar Dinkin Dunia.

Saidai yan adawa da yan tawaye, sun yi watsi da wannan mataki.

Tunni har ma ya tawaye sun nada madugun su, Guillaume Soro a matsayin Pramintan rikwan kwarya mai cikkaken mulki, sun kuma zargi masu shiga tsakanin rikicin na kasar Kote Divoire, da nuna daurin gindin ga shugaba Lauran Bagbo.