1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akalla mutane dubu 2 da 700 suka rasu a girgizar kasar da aka yi a Indonesia

May 27, 2006
https://p.dw.com/p/BuwW
Yawan wadanda suka rasu sakamakon mummunar girgizar kasar da ta auku a tsakiyar tsibirin Java dake kasar Indonesia yanzu ya kai akalla mutane dubu 2 da 700. Jami´an gwamnati sun ce wasu dubun dubatan mutane kuma sun samu raunuka a wannan girgizar kasa wadda karfin ta ya kai awo 6.2 a ma´aunin Richter. Girgizar kasar ta auku da misalin karfe shida na safe agogon yankin. Jami´ai sun ce girgizar ta fi karfi a wani yanki mai nisa kilomita 30 kudu da birnin Yogyakarta mai dadadden tarihi. Gidaje da dama sun rushe yayin da aka samu katsewar wutar lantarki da kuma wayoyin tarfo kana kuma an rufe filin saukar jiragen sama dake birnin. Bugu da kari kasa ta motsa sau da yawa bayan girgizar. A dai halin da ake ciki hukumomi na sa ido akan aman wutar da dutsin Merapi dake kusa ke yi, wanda ake fargabar cewa girgizar kasar ka iya shafar aman wutar.