1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akwai rashin kula ga harkar lafiya a Afirka

Usman Shehu Usman
September 1, 2017

Shugaban hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce zai hada kan shugabannin Afirka ta yadda za su kyautata harkokin kiwon lafiyar kasashensu don magance gibin da ke a fannin a nahiyar.

https://p.dw.com/p/2j95Y
Tedros Adhanom Ghebreyesus ehem. Außenminister Äthiopien
Hoto: DW/T. Woldeyes

Wannan  yunkuri na shugaban Hukumar Lafiya wato WHO, na zuwa ne dai dai lokacin da ake ci gaba da zargin shugabannin kasashen Afirka da rashin maida hankali ga harkokin kiwon lafiya, yayin da su kuma, suke zuwa jinya a manyan kasashen ketare. Matsayin shugaban hukumar kan ankarar da shugabannin Afirka, dangane da muhimmancin inganta harkar kula da lafiya na Afirka, ya bayyana shi ne lokacin wani taron da ya hada ministocin lafiyan kasashen na bakar fata, wanda aka yi a kasar Zimbabuwe.

Mr. Tedros Adhanom Ghebreyesus wanda dan asalin kasar Habasha ne, ya bayyana cewa yanzu lokacin fada wa juna gaskiya ne kan irin sakacin da shugabannin wasu kasashen ke yi da fannin lafiya, wanda hakan kai tsaye yake shafar talakawa, saboda ganin su masu iko suna ketarawa zuwa manyan kasashe a duk lokacin da bukatar jinya ta taso.

"Na ziyarci kasar Yemen, a can na ga wata uwa da ke tare da wata ‘yar ta da ke cikin yanayi mai munin gaske. Sai da suka yi tafiyar sa’o’i masu yawa suka sami isa wani asibiti. Ina gani matar nan take ta fara rokon likitoci su taimaka su ceto mata ’yar tata. A nan ne a hakika hankali na ya dawo kan wannan gaskiyar da na ke fada maku cewar tilas ne fuskance ta".

A bayyane ta ke dai wadannan munanan yanayi da jama’a ke ciki na da tarin yawa a galibin kasashen Afirka ba Yemen ce kadai ke da su ba, al’amarin da sakaci na mahukunta ga aikin kula da lafiya ke zama musabbabi. Abin da shugaban hukumar lafiyan ya ce, dole a tashi don magance shi.

Kenia Kenyatta National Hospital - Krankenhaus in Nairobi
Hoto: Getty Images/AFP/S. Maina

"Fifita himma ga tsarin lafiya zai kasance abu mafi muhimmanci. Kama daga ma’aikata zuwa samar da kayayyakin aiki , abin da zai samar da nagarta kenan a alkiblar da muka dosa. Wani abin kuma shi ne samun ingantattun bayanai da ilimin zamani ke dauke da su, sai kuma jagorancin kwarai ta fannin cibiyoyin kula da lafiyar jama’a. Samu tare da amfani da wadannan abubuwan da na zayyana, su ne za su tabbatar mun dauki hanya ta kwarai"

Tarin matsalolin da ke asibitocin kasashen Afirka da rashin kula ke musabbabi, ya tilasta shugabannin kasashen nahiyar fita a kai a kai, zuwa kasashen waje don yin jinya inda suke ganin can ne ke da tabbas. A cikin wannan makon ne dai aka jiyo ministan lafiya na kasar Afirka ta Kudu, na sukar jagororin kasashen na Afirka, wadanda ya ke cewa ba kananan kudade suke barnatawa zuwa jinyar da suke yi a manyan kasashen ba, kudaden da yace a wasu kasashen sun kai yawan kasafin kudin kula da lafiya da aka ware ga kasar baki daya.

Ministan lafiyan Afirka ta Kudu kenan Aaron Motsoaledi ke cewa "bana jin dadin kasancewar Afirka ce kadai nahiyar da shugabanninta ke zuwa wasu nahiyoyi don neman magani. Hakan ba misali ba ne mai kyau, don lokacin kawai da za mu iya cewa komai na tafiya dai-dai, to shi ne lokacin da su shugabannin na karbar jinya a nan nahiyar Afirka.

Kusan dukkanin shugabannin kasashen na bakar fata, irinsu Robert Mugabe na Zimbabuwe da Muhammadu Buhari na Najeriya da tsohon shugaban kasar Angola Jose Eduardo dos Santos, mutane ne da ke gaba wajen ketarawa wajen nahiyar don neman magani a rashin lafiya da suke fuskanta.

Masana dai na ci gaba da cewa, batun kulawar bai daya ta lafiya, batu ne da zai ci gaba da zama kalubale, muddin ba a sake salo aka yi shigen yekuwar da shugaban Hukumar Lafiyar Duniyan ya yi a yanzun ba.