1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alámura na ƙara taɓarɓarewa a Dafur

October 6, 2006
https://p.dw.com/p/BuhE

Sakataren Majalisar ɗinkin duniya Kofi Annan ya baiyana cewa halin da ake ciki a yankin Dafur na ƙasar Sudan ya doshi kaiwa ga kaiwa ga mummunan balaí. A rahoton da ya kan gabatarwa Majalisar duniyar wata wata kan yanayin da ake ciki a Dafur, Annan yace tarzoma da fyaɗe da rashin tsaro sai ƙara taázzara suke kulli yaumin a yankin duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma tsakanin gwamnati da ɗaya daga cikin kungiyoyin yan tawayen. Ana cigaba da fuskantar arangama da ɗauki ba daɗi tsakanin yan tawaye da mayaƙan sa kai da kuma yan banga duk da shawarar fadar khartoum na tura ƙarin sojoji zuwa Dafur din. Ita dai fadar khartoum, ta ƙi amincewa da sojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar ɗinkin duniya su karbi ragamar gudanarwar shaánin tsaro daga hannun dakarun ƙungiyar gamaiyar Afrika waɗanda ke fama da matsalar rashin kuɗi na tafiyar harkokin rundunar sojin. Kofi Annan yace idan har shaánin tsaron bai inganta ba, to kuwa akwai yiwuwar cewa ƙasashen duniya za su fuskanci gagarumin ƙalubale na aikin taimakon jin kan alúma.

Ƙasar Amurka ta buƙaci kwamitin tsaron na Majalisar ɗinkin duniya, ya maida martani ga kashedin da Sudan ta yi cewa dukkan wata ƙasa da ta yi alƙawarin bada gudunmawar soji ga rundunar kiyaye zaman lafiyar na Majalisar ɗinkin duniya a Dafur, ta ƙudiri aniyar zalunci ne da ƙoƙarin mamaye ƙasar.