1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alúmar kasar Kenya sun ki amincewa da sabon daftarin kundin tsarin mulki

November 22, 2005
https://p.dw.com/p/BvK4

Mafi akasarin alúmar kasar Kenya sun ki amincewa da sabon daftarin kundin tsarin mulkin kasar. Sakamakon farko da aka samu na kuriár raba gardamar ya nuna mazabu 131 daga cikin 210 sun kada kuriár rashin amnanna da daftarin kundin tsarin mulkin, lamarin dake zama babban koma baya ga shugaban kasar Mwai Kibaki. Hukumar zaben kasar Kenyan ta baiyana cewa ya zuwa yanzu wadanda ke adawa da kundin tsarin mulkin na da kashi 49 cikin dari na adadin kuriún yayin da kuma masu goyon bayan daftarin suka sami kashi 33 cikin dari na yawan kuriún. Jamaá da dama a kasar na daukar kuriár raba gardamar a matsayin wani mataki na nuna rashin goyon baya ga gwamnatin wadda suka ce ta gaza magance matsalar cin hanci da rashawa da ya yiwa kasar katutu. Sabon daftarin tsarin mulkin shi ne na farko tun bayan da kasar ta sami yancinkai a shekarar 1963.