1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

140710 Megacitys Kairo LANG

October 24, 2010

Mazauna birnin Alƙahira sun ƙware wajen sajewa da kowane irin halin rayuwa da aka shiga mai daɗi ko maras daɗi ga zamantakewar al'uma.

https://p.dw.com/p/PmWP
Komai a yamutse a birnin AlƙahiraHoto: picture-alliance/dpa

Birnin Alƙahira na ƙasar Masar wani birnin ne mai fuskoki kimanin dubu ɗaya. A hukumance babban birnin na Masar yana da yawan mutane kimanin miliyan 16, amma mazauna birnin na da imanin cewa yawan mutane da ke a birnin ya zarta wannan adadin. Tuni dai babban birnin na ƙasar Masar ya shiga jerin manyan biranen duniya da ake yiwa laƙabi da Mega Cities, musamman dangane da girmansa da yawan al'umma daban-daban da ya ƙunsa.

Alƙahira babban birnin ƙasar Masar, birni ne da ya cika da jama'a daban-daban. Birnin dai na da dadaɗɗen tarihi mai yawan gaske kuma saboda haka birnin na Alƙahira ke ci-gaba da zama wani abin sha'awa da burgewa ga mawallafan ƙasar ta Masar. Cikinsu kuwa har da Belal Fadl matashin mawallafin ƙasar wanda ke ƙaunar yanayin cunƙoso a birnin amma a lokaci guda kuma yake ƙinsa.

Megacities Ägypten Autor Belal Fadl
Mawallafin ƙasar Masar Belal FadlHoto: DW/Hafez

“A gare ni birnin Alƙahira tamkar tumbin giwa ne, da zarar na dira ciki, ina iya samun abubuwan da nake buƙata ga littattafai na. Alal misali wani mai sayar da jaridu wanda na taɓa rubuta littafi kansa, ai yana nan, yana sayar da jaridunsa a kusa da gida na. Salon sayar da jaridarsa iri ɗaya ne, ko jaridun goyon bayan gwamnati ne ko na suka. A gare shi dukkansu maƙaryata ne. Yana rayuwa ne da wannan sana'a.”

Gidajen shan shayi da gahawa a hankalin mawallafa

Belal Fadl na sha'awar zuwa wani gidan shan gahawa Café Riche a birnin na Alƙahira inda masu ji da kansu a birnin ke haɗuwa. A cikin shekarun 1960 mashahuriyar mawaƙiyar nan ta Masar wato Umm Kalthoum ta yi bikin waƙoƙi da raye-raye da yawa a wannan gidan shan gahawa.

Bayan ya kurɓa gahawa Belal Fadl ya fara da ba da labari game da mazauna wannan babban birni, wato rayuwarsu, matsalolinsu da kuma irin gwagwarmayar da suke sha. Ya fi mayar da hankali kan talakawa. A cikin littafinsa mai taken: "Al Sukkan Al Assleyan le Masr" wato ‘yan asalin Masar, mawallafin ya bambamta tsakanin talakawa da ‘yan gata a Masar waɗanda su ne suke cin gajiyar arzikin wannan ƙasa, wato ‘yan kasuwa, ministoci da kuma mawallafa irinsa.

“Ina tunani akan yadda Masarawa ko kuma in ce gwamnatin Masar take nesa da ainihin abubuwan da mutanenta ke buƙata. A hannu ɗaya dole mutane kamar wannan mutumin dake sayar da jaridu, su warware matsalolinsu na yau da kullum. Sannan a ɗaya hannun gwamnati tana mayar da hankalinta kan wasu batutuwa na daban. Ina mai ra'ayin cewa a matsayi na na mawallafi na yi sa'a. Idan an haife ka a ɗaya daga cikin waɗannan birane wato Alƙahira ko Istanbul. Domin mawallafa a wasu biranen na shan wuya wajen samun abubuwa masu sha'awa da za su wallafa littattafai a kai. A waɗannan birane biyu da ka hau kan titi za ka samu dukkan abubuwan dake ke buƙata na rubuta littafi.”

Sabon salon rubutun adabi kan Alƙahira

Armenviertel in Kairo Slum in der äyptischen Hauptstadt Kairo
Unguwar talakawa a AlƙahiraHoto: picture-alliance/dpa

A cikin shekaru 10 da suka gabata an shiga sabon yanayi a fagen adabi a Alƙahira, inda sabbin mawallafa suka fara rubuce-rubuce a game da birnin wanda suka tsana amma a lokaci ɗaya kuma suke ƙauna. Suna bayani game da kyawawa da munanan ɓangarori na birnin. Da yadda gwamnati ta kasa cika buƙatun al'umma, da yadda take fatali da matsalolin ƙasa. Waɗannan rubuce-rubuce ka iya ta da rashin fahimta inji Belal Fadl. To amma ya ce muryarsu tana tashi. Da bayani ya yi nisa; Belal ya karanta wani sashe na wani littafi da ya rubuta game da wata zanga-zangar matasa da ke adawa da ƙarancin albashi da tashin farashin kaya a ranar 6 ga watan Afrilun shekarar 2008. An kame da yawa daga cikinsu a dangane da haka aka kafa wata ƙungiya mai suna “Matasan 6 ga watan Afrilu.”

“Zan yi tattaki zuwa wajen shugaban ƙasa. Na shiga cikin jerin zanga-zanga. Ba zan ƙaryata haka ba. Wataƙila na yi kuskure da na shiga cikin zanga-zangar, to amma da me ya kamata in yi? Kamar sauran ‘yan ƙasa, ni ma mawuyacin hali da Masar ke ciki ya kai min iya wuya. Mun gudanar da zanga-zanga ne da fatan hukumomi za su fahimci halin da muke ciki, za su daƙile hauhawar farashin kaya. Mun yi zanga-zanga ne domin su faɗa mana yadda iyayenmu za su iya bamu tabbacin samun kyakkyawar rayuwa duk da cewa albashinsu kaɗan ne. Ta yaya za mu samu makoma mai kyau yayin da ba mu koyi wani abin a zo a gani a makarantu da jami'o'i ba? Mun yi zanga-zanga amma ba mu yi tashin hankali ba. Shin kun yi imani za mu yi ta yajin aiki ko zanga-zanga a kullum, in da mun gamsu da halin da muke ciki?”

Manufar irin waɗannan rubuce-rubuce shi ne sukar lamirin gwamnati, wani ɓangare kuma shi ne na barkwanci da ba'a. Barkwanci dai na taka muhimmiyar rawa a tsakanin Masarawa. Mawallafa a Masar dai sun sha yiwa shugaba Hosni Mubarak da gwamnatinsa shaguɓe a littattafansu.

Deutsch ägyptische Modenshow in Kairo
Bikin kayan sawa na zamani a AlƙahiraHoto: Alaa Abdelbary

“Ina kwance akan gadon asibiti da ankwa a hannu na, bayan an kama ni. Yanzu na san abin da nake so. Ba na son wani adalci na zamantakewa ko wani ‘yanci. Haka nan ba na son wani sauye sauye na siyasa. Me nake so, ya shugaban ƙasa, yanzu da ka kwance min ankwa kuma ina iya sosa jiki na?”

Irin wannan salon rubuce-rubucen ya sa Belal Fadl ya shahara musamman tsakanin matasa masu karance karance. Kawo yanzu ya wallafa littattafai guda biyar waɗanda dukkansu kuma suka yi kasuwa.

“Masarawa mutane ne da suka iya barkwanci. Da haka suke iya mantawa da mawuyacin halin da suke ciki. Gatse ko ba'a wani ɓangare ne na al'adar Masar. Wato kamar wasan kwaikwayo a tsakanin Indiyawa ko mawallafan Mexiko masu rubuce rubuce akan fina-finai na ban tsoro.”

Kowane sashe na jama'a a cikin Alƙahira

A duk inda mutum ya zaga a birnin zai ga tarin jama'a, yara, tsofaffi, mata cikin lulluɓi da na zamani, Turawa da ‘yan Asiya masu ‘yanwon buɗe ido, msu saye da sayarwa da kuma uwa uba cunƙoson motoci da ba ya taɓa ƙarewa. To ka yaya Belal Fadl ya ke iya rabe zare da abawa a cikin wannan yamutsi?

Megacitys Kairo
Birnin Alƙahira na da lunguna daban-dabanHoto: DW

“Na san kowane lungu da saƙo na birnin Alƙahira. Duk da cewa a birnin Alexandriya aka haife ni, amma iyaye na ‘yan Alƙahira ne. Ina ƙaunar dukkan abubuwa marasa kyau na wannan birni, wato kamar cunƙoson motoci da gurɓatacciyar iska. Ina jin daɗin ganin cewa bana samun tsabtatacciyar iskar shaƙa a Alƙahira saboda hayaƙin motoci. Idan wata rana aka wayi gari an tsabtace wannan birnin to ka ga ba zan iya gane shi ba kenan. Ya ƙunshi abubuwa da suka saɓa da juna, munana da kyawawa. Mutanen wannan birnin sun tsara rayuwarsu yadda za ta dace da waɗannan abubuwan.”

Muhimmin abun ga wannan sabon salon adabi tsakanin sabbin jinin mawallafan na Masar shi ne sun fi mayar da hankali ne kan batutuwa na siyasa da sauyin zamantakewa.

Mawallafa: Hebatallah Ismail / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal