1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alƙiblar gwamantin Jamus

July 21, 2010

Angela Merkel ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnatinta duk da ƙalubalen da ta ke fiskanta.

https://p.dw.com/p/OQrR
Angela MerkelHoto: AP

Shugabar gwamantin Jamus ta nunar da cewa ƙasarta na samun ci gaba mai ma'ana duk da matsin tattalin arzikin da ke addabarta. A wani taron manaima labarai da ta gudanar a birnin Berlin, Angela Merkel ta ce bunƙasar tattalin arziki da Jamus ta samu a 'yan watannin na, ta zarta hasashen da aka yi da farko.

Merkel ta yi kuma amfani da tattaunawa da 'yan jarida da ke zama na ƙarshe kafin tafiyarta hutu, wajen jadadda aniyarta ta aiwatar da muradun da gwamantinta ta sa a gaba, duk ma ƙalubalen da ta ke fiskanta. Shugabar gwamantin ta Jamus ta ce za ta ci gaba da bai wa fannin ilimi fifiko duk da murabus wasu daga cikin kusoshin jam'iyarta ke fiskanta.

 Kididdigar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar ta nunar da cewar, farin jinin Angela Merkel yayi  raguwar da ba taba ganin irinsa ba tun shekaru 24 da suka gabata. Hasashen dfa aka gudanar ya nunar da cewa jam'iyar CDU ta Angela Merkel na iya shan kayi idan aka gudanar da zaɓe cikin 'yan watannin nan masu zuwa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu