1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

al-Assad na son kura ta lafa a Syriya

Mouhamadou Awal BalarabeMarch 1, 2016

Duk da cewa har yanzu ba a mutunta yarjejniyar tsagaita wuta yadda ya kamata, amma shugaba Bashar al-Assad na mafarkin ganin wannan mataki ya fara aiki a Syriya.

https://p.dw.com/p/1I591
Syrien Präsident Bashar al-Assad Interview
Hoto: picture alliance/dpa/SANA

Shugaban Bashar al-Assad na Syriya ya yi alkwarin tsayawa a kan kafafunsa don ganin cewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin Amirka da Rasha ta ci gaba da aiki a kasarsa. Cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin mallakar gwamnatin Jamus wato ARD, al-Assad ya yi tayin yafe wa duk 'yan bindigan Syriya da za su ajiye makamansu.

A halin yanzu dai gwamnatin Syriya da kuma bangaren tawaye na ci gaba da zargin junansu da rashin mutuntu yarjejeniyar tsagaita wuta sau da kafa. Ko da ita ma Rasha sai da ta bayyana cewar fadar mulkin ta Damascus ta saba wa wannan yarjejeniya so 15 a yankunan Homs da Aleppo a cikin sa'o'i 24 na bayan-bayannan.

Sai dai shugaban na Syriya ya ci ba kamshi gaskiya a ciki, inda ya ce "'Yan tawaye ne suka saba wa wannan yarjejeniya tun sa'o'i farko bayan da ta fara aiki. Alhali dakarun gwamnati sun yi iya kokarinsu don ganin cewa sun mutuntata."