1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Bashir ya yi tofin Allah tsine ga ƙasashen yammacin Duniya.

April 10, 2010

Shugaban Sudan ya ce, ba zai ´kyale ƙasashen yammacin Duniya su ci zarafin ƙasar sa ba

https://p.dw.com/p/MsOE
al-Bashir yana rajistar katin zaɓeHoto: picture alliance/dpa

A jawabin da ya yiwa magoya bayan sa wajen kammala yaƙin neman zaɓe, shugaban Sudan Umar Hassan al-Bashir ya yi Allah wadai da kotun Duniya dake shari'ar manyan laifukan yaƙi, wadda ta bayar da sammacin cafke shi. Shugaba al-Bashir ya ambata cewar:

" Alƙawarin da muka ɗauka shi ne ƙin kyale ƙasashen yammacin Duniya su yi karan tsaye ga martabar ƙasar mu, ko ta hanyar asusun bayar da lamuni a Duniya ne, ko kuma ta hanyar kotun ƙasa da ƙasa dake hukunta masu aikata manyan laifukan yaƙi ne."

Shugaba alBashir ya yi wannan kalamin ne ga magoya bayan sa a yankin Umm Badda a lokacin rufe yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar da muhimman masu ƙalubalantar sa suka janye daga ta'karar, wadda suka yi zargin cewar ba za'a yi adalci ba.

Tsohon Frime Ministan Sudan Sadiq al- Mahdi ya janye daga takarar, a yayin da ita tsohuwar ƙungiyar 'yan tawayen SPLM kuwa ta ce zata janye daga zaɓukan da za'a yi a ɗaukacin yankunan dake arewacin ƙasar, in banda Niilul Azraq da kuma ƙudancin Kordufan.

A gobe Lahadi ne - idan Allah ya kaimu al'ummar Sudan ke zuwa runfunan zaɓe domin ka'ɗa ƙuri'a.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Muhammad Nasir Auwal