1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AL-Maliki yana samun rata

March 14, 2010

Jam'iyu masu ƙawance da firayim minista Nuri-Almaliki, suna samun galaba kan abokan hamayya

https://p.dw.com/p/MSR8
Jawad al-Maliki,Hoto: AP
Jam'iyu masu ƙawance da firayim minista Nuri-Almaliki, suna kan gaba a sakamakon zaɓen ƙasar Iraƙi, abinda ya ba shi damar samun 'yar rata tsakaninsa da abokin hamayyarsa wanda suke gogayya a birnin Baghadaza. Sakamakon farko da hukumar zaɓen ƙasar ta bayar, ya nuna masu gawance da Al'maliki sun zarce da ƙuri'u dubu 60 a dukkan faɗin ƙasar a kan abokan hamayyarsu. Jam'iyar 'yan riƙau ta masu bin shi'a ita ta zo ta uku a zaɓen. Izuwa yau da rana ne ake saran samun sakamakon wushin gadi, sati guda bayan da aka gudanar da zaɓen 'yan majalisa mai wakilai 325. Mawallafi: Usman Shehu Usman