1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Qa´ida a Iraƙi ta yi barazanar kaiwa kamfanonin Sweden hari

September 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuBN

Kungiyar al-Qaida a Iraqi ta sake yin barazanar kashe karin shugabannin ´yan sunni wadanda ke bawa Amirka ko kuma gwamnatin Iraqi hadin kai. A cikin wani sako da ta watsa ta yanar intanat kungiyar ta kuma yi ikirarin kisan shugaban ´yan sunni Abdul Sattar Abu Risha wanda aka yiwa kisan gilla a ranar alhamis saboda ba da hadin kai ga Amirka a yakin da take yi da masu matsanancin ra´ayi. A wani labarin kuma shugaban kungiyar al-Qaida a Iraqi Abu Omar al-Baghdadi ya yi tayin ba da ladar dala dubu 100 ga duk wanda ya kashe mai zanen ban-dariya na kasar Sweden Lars Vilks a dangane da wani zaben batanci da yayi na Annabi Mohammad (SAW). Al-Baghdadi ya kuma yi barazanar kaddamar da hare hare kan kamfanonin Sweden idan kasar ba ta nemi gafara ba.