1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al Shabaab ta kashe sojojin Somaliya 61

June 8, 2017

Rayuka da dama ne suka salwanta a wani harin da mayakan tawayen Al shabaab suka kaddamar kan sansanin soji da ke yankin Puntlad na kasar Somaliya.

https://p.dw.com/p/2eKsE
Somalia Al-Shabaab Kämpfer
Hoto: picture alliance/AP Photo/F. A. Warsameh

Sabbin bayanan da ke fitiwo daga yankin, sun ce sama da mutane 60 ne suka mutu a artabu tsakanin sojojin gwamnati da mayakan na Al Shabaab. Mayakan na Al Shabaab sun kuma yi awon gaba da wasu motocin sintiri na sojojin ta re da kone wasu kurmus.

Galibin wadanda suka mutu dai jami'an sojin ne kamar yadda Al Shabaab din ta yi ikirari. Sai dai kamar yadda gwamnan yankin Bari, Yusuf Mohamed ya tabbatarwa kamfanin labaran Reuters, ba a kai ga tabbatar da yawan wadanda suka mutu ba, sai dai ya shaidar da kasancewar sojoji a sansanin da ya fuskanci harin.