1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

al-Shabaab ta yi kashe-kashe a Somaliya

November 28, 2016

Rahotanni daga Somaliya na cewa akalla mutane 30 sun mutu a wani taho mugama tsakanin mazauna kauyen Dumaaye da mayakan al-Shabab.

https://p.dw.com/p/2TNov
Somalia Autobombenanschlag in Mogadischu
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Y. Warsame

Wannan artabun ya faru ne biyo bayan martanin kare kai na wani matakin tilasta biyan haraji da 'yan tada kayar bayan suka kakaba wa mazauna yankin. Hukumomin tsaro a Somaliya sun tabbatar da kashe 'yan bindigan 26, tare da wasu fararen hula da manoma da suka fafata da mayakan na al-Shabaab.

kawo yanzu dai babu martani daga bangaren mayakan al-Shabaab kan wannan sabon hari, amma a baya dai sun sha daukar alhakkin munanan hare-hare da ke sanadiyar rayuka da dama, tun bayan da suka lashi takobin kalubalantar gwamnatin Somaliya. Tuni dai aka dauki matakan kara jibge jami'an tsaro a kauyen Dumaaye don kare mazauna yankin.