1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alamar rudani a jadawalin zaben Nijar

Abdolaye Mamane Amadou/USUMarch 2, 2016

Wasu kungiyoyin kare hakkin jama'a da demukradiya sun soma nuna damuwarsu kan yanda jadawali hukumar zabe ta CENI na zabukan shugaban kasa karo na farko da na biyu ke shirin saka kasar a yanayi na rashin tabbas.

https://p.dw.com/p/1I5hN
Niger Präsidentschaftswahl Ergebnisse
Hoto: DW/K. Gänsler

Kungiyoyin na la’akari ne da dokoki da ka’idodin tsarin zabe har ma da na kundin tsarin mulkin kasar, kan wa’adin da ya tanada da halin da ake ciki yanzu a zahiri. Malam Moussa Tchangari sakataren kungiyoyin Alternative Espace Citoyen wani dan rajin kare hakin jama'a da demukradiya shi ne ke bayyana matukar fargabarsa kan halin da ake kan hanyar tsunduma a ciki na rashin ka’ida, dangance da dokokin tsarin mulki da na zabe biyo bayan zaben shugaban kasa zagaye na farko da aka gudanar dama bayyana sakamakonsa da hukumar zabe ta yi a karshen watan jiya.

Tchangari na la’akari ne da ayoyin dokar zabe da ke baiwa 'yan takara da jam’iyyun siyasa wa’adin tsawon kwanaki 15 don kai karar sakamakon zaben da hukumar zabe ta wallafa a ranar jumu’a 26 ga watan jiya a gaban shari’a, tare da wasu karin kwanaki 7 don baiwa wadanda aka zarga damar kare kai kafin daga bisani kotun ta tsarin mulki ta wallafa sakamakon ya kasance na dindindin. Wanda hukumar zabe za ta iya amfani da shi don sake kiran wani yekuwar gangamin zabe a zagaye na biyu.

Abubuwan da dan gwagwarmayar yace idan har aka yi wa wadannan dokokin biyayya to ba shakka hakan zai kai ga taba wa’adin mulkin shugaban kasar da yakamata ya kawo karshe a ranar 6 ga waran Aprilu da misalnin karfe 12:00 na dare. Yace idan har ba’ayi zaben ba a wannan lokacin kamar yadda hukumar zabe ta wallafa to bas hakka w’adin shugaban kasa zai wuce wannan lokaci kenan, ma'ana za’a taka doka domin ita doka ta hana haka saboda sun lura da akwai wannan sai dai takan yiwu tunaninmu ba daya yake da saura.

Moussa Tchangari, Journalist und Menschenrechtler
Moussa Tchangari, Dan fafitikaHoto: DW/ Thomas Mösch

Suma dai wasu jigajigan 'yan siyasar kasar da suka shiga takara a zaben na shugabancin kasa da ya gabata irinsu Alhaji Abdou Labo sun tabbatar da sanin halin da jadawalin zaben na hukumar zabe yake ciki a yanzu, to amma kuma sunce su masu biyar doka ne saboda hakan hukumar zabe ita ce ke da wuka, ita ke da nama kan duk wani w’adin da ta dauka na tunkarar zaben. Labo yace duk wadannan jadawalin da kuke ganin CENI it ace tabi dalla-dalla, to yanzu zuwa gaba idan abin ya kawo gardama 'yan siyasa da gwamnati da yan kasa sune idan har akwai wasu kurakurana da yakamata a kawowa gyara fuska to CENI yakamata ta shiga gaba ta kawo.

Da yake mayar da martani kan wannan batu wakilin jam’iyyar PNDS Tarayya a hukumar zabe Boubacar Sabo ya tabbatarwa DW cewar wannan matsalar ba za ta haifar da wani tarnaki ga gundaren zaben bana. inda yace bai taba komai babu wani abun da za’ayi daman zagaye na biyu, cewa aka yi yakin neman zabe zai fara ne daga ranar da kotun tsarin mulki ta wallafa sakamakon dindindin, saboda hakan ba’a fadi kwanaki ba da yanda za’ayi har zuwa jajibirin zaben yana iya zama kwana biyu, uku ko kwana shidda, shi ne aka ce ba’a tsaida ranar yakin neman zabe ba. Yanzu su ne za su shiga wurin kotun tsarin mulki su rinka fading a wa’adi da kotu za ta dauka.

Hukumar zabe dai da wakilin DW ya tuntube su, ta bakin kakakinta cewa ta yi wa’adin da take aiki da shi shi ne na jadawalin da ta wallafa wa al’umma, saboda hakan komai rintsi komai wuya za ta kiyaye. Sai dai hukumar na tabbatar da hakan ne a yayin da a share daya har yanzu kotun ta tsarin mulki ba ta ce uffan ba kan sakamakon zaben, sakamakon da ba shakka idan har ya kai tsawon kwanaki 15 zai iya sake bude wani sabon babi na hayaniyar siyasa da kai wa intaha dinsa, zai dauki wani lokaci.