1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alamar samar da zaman lafiya Juba

Usman Shehu UsmanApril 13, 2016

Bisa ga dukkan alamu an kama hanyar warware rikicin kasar Sudan ta Kudu wanda ya jawo yakin basasa inda dubban mutane suka mutu

https://p.dw.com/p/1IUIM
Südsudan Waffenstillstand 01.02.2014 Addis Abeba
Hoto: Reuters/T. Negeri

Mataimakin shugaban kungiyar 'yan tawayen kasar Sudan ta Kudu ya koma Juba babban birnin kasar a bisa tsarin samar da zaman lafiya da aka cimma. Alfred Ladu Gore da saukan sa a juba, ya fadawa manema labarai cewa ya iso Juba ne domin tabbatar da cewa zaman lafiya da aka cimma zai dore, ba tare da kawo cikas ga yarjejeniyar da aka yi ba. Wannan dai share hanya ne na komar shi kansa madugun 'yan tawaye wanda yanzu aka sake mai do masa da mukamin mataimakin shugaban kasa, wanda da ma can ya rike kafin a kore shi, abinda ya kuma ya jawo barkewar yakin basasa. Ana dai saran Riek Machar zai koma Juba da zimmar kafa gwamnatin hadaka, wanda shugaba ASalva Kiir ya amince a kafa bisa matsin lamba daga kasashen duniya.